Majalisar wakilai ta gayyaci shugaban kwastam kan sayar da motoci, Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Kanal Hameed Ali (mai ritaya).
Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da kararrakin jama’a ya gayyaci babban Kwanturolan Hukumar Kwastam, Hameed Ali, dangane da sayar da motoci a matsayin tarkace da hukumar ta yi.
An umurci Ali da ya bayyana a zauren majalisar a ranar Talatar da ta gabata sakamakon gazawarsa zuwa ranar Larabar da ta gabata.
Gayyatar ta biyo bayan koken da shugaban kungiyar masu sayar da gwanjo ta Najeriya Alhaji Musa Kurra ya gabatar ga kwamitin.
PUNCH ta bayyana cewa an sayar da ɗaruruwan motocin da hukumar kwastam ta kama daga hannun masu fasa ƙwauri a kan farashin kasuwa ta hanyar abin da NCS ta kira rabon gwanjon kai tsaye.
A cigaba da wallafawa, NCS ta gayyaci Kurra da ya gurfana a gaban wani kwamiti a ranar 8 ga watan Nuwamba tare da takardu domin dakile zarge-zargen da ya yi wa hukumar.
Sai dai Kurra bai mutunta wannan gayyata ba, inda ya bayyana cewa hukumar ba ta da hurumin yi masa kiranye, yana mai jaddada cewa kamata ya yi ta magance zargin sayar da kadarorin da aka kama ba tare da bin ka’ida ba.
A cikin sammacin, an umurci Ali da ya bayyana a gabansa dauke da takarda mai laushi da kwafi 10 na takaitaccen bayaninsa na sayar da motocin da aka kama ta hanyar yin gwanjon kai tsaye.
Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin, Jerry Alagbaoso, mai suna, ‘Nigeria Association of Actioneers (mai shigar da kara) kan hukumar kwastam ta Najeriya kan hada-hadar sayar da kayan gwanjo kai tsaye da sauran kayayyaki.
Ya kara da cewa, “Duk da bukatar da aka ambata a sama tana nan a gaban wannan kwamiti kuma bayanan koken da aka ambata sun riga ka sani, alhali an sanya koken da kwamitin ya saurara domin tantancewa.
“A nan ana bukatar ku lura da sashe na 88 da 89 (c) na kundin tsarin mulkin mu (kamar yadda aka gyara) sannan ku bayyana gaban wannan kwamiti a ranar Talata 29 ga watan Nuwamba, 2022 da karfe 2 na rana ko kuma nan da nan kamar yadda kwamitin zai ba da umarni.
Da fatan za a kula da ka’idojin NCDC. Wuri: Majalisar Wakilai Room 429 (sabon reshe).
“Za ku gabatar da kwafi guda ɗaya da kwafi 10 na taƙaitaccen bayanin ku.
Kuma a kara lura cewa idan ba ku halarci zaman ba kamar yadda ake bukata, za a iya sauraron karar ko kuma a tantance idan ba ku nan.”
Rahoto: Salma Ibrahim Ɗan-ma’azu Katsina.