Shugabannin kasashen Afrika sun jinjinawa shugaban Kasa Buhari bisa kyajkyawan jagorancin a Najeriya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a cikin wannan mako, ya lashe zukatan ’yan uwansa shugabannin Afirka a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, inda suka yi ta ba da shaida masu kyau na halayen shugabancinsa.
Majiyar Dimokuradiyya ta bayar da rahoton cewa, shugabannin kasashen Afirka sun je birnin Yamai ne domin halartar taron kolin bunkasa masana’antu da habaka tattalin arzikin kasashen Afirka, da kuma wani zama na musamman kan yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA).
Shugabannin kasashen Afirka sun yi amfani da damar taron wajen halartar bikin kaddamar da littafin ‘Muhammadu Buhari: The Challenges of Leadership in Nigeria’, wato kalubalen shugabanci a Najeriya wanda ya gudana a Yamai.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin, shugaba Mohamed Bazoum na jamhuriyar Nijar ya bayyana shugaban na Najeriya a matsayin ‘‘mutumin da ba shi da ra’ayin mazan jiya, mutum ne mai tawali’u, mai kishin kasa kuma mai kishin demokradiyya”.
Ya kuma yaba wa marubucin littafin, Farfesa John Paden, kan yadda ya yi rubuce-rubuce kan rayuwa da ayyukan shugaban Najeriya.
Paden Farfesa ne na Nazarin Kasa da Kasa a Jami’ar George Mason, da ke Arewacin Virginia, a Amurka.
Jim kadan bayan isowarsa birnin Yamai a ranar Alhamis, Buhari ya kaddamar da wani katafaren titi Boulevard mai fadin kilomita 3.8 da 160 da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanyawa sunan sa.
Shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Embaló, wanda kuma shine shugaban kungiyar ECOWAS a halin yanzu, ya shaidawa wadanda suka halarci taron cewa, ana kiran mahaifinsa Muhammadu kuma an haife shi a shekara daya da Muhammadu Buhari. (NAN).