Sojan Najeriya ya Bindige Laftanar kusun da guda da abokanan aikinsa su uku a Sokoto.
Wani sojan Najeriya, mai suna Lance Nwobodo Chinonso, wanda ake zargin ya kashe abokan aikinsa guda uku da suka hada da Laftanar Sam Oladapo, Kwamandan Rundunar Sojoji (FOB), Rabah, a jihar Sokoto, inji rahoton TheGuardian.
A rahoto na cewa Chinonso ya bude wuta kan Lt. Oladapo, babban jami’in hukumar FOB, Sajan Manjo (CSM), Sgt. Iliyasu Inusa, da dai sauransu nan take suka Mutu.
ALFIJIR HAUSA ta tattaro cewa; inda Sojan da ya tafka wannan ta’asar ya mayar da bindigar ga kansa kuma ya kashe kansa nan take bayan ya kashe abokan aikin.
Wani babban jami’i a sashin Sokoto ya ce an kai gawarwakin wadanda aka kashe zuwa asibitin koyarwa na Usmanu Danfodiyo (UDUTH), Sokoto, yayin da aka fara bincike.
Ya bayyana cewa; mai yiwuwa sojan ya kasance yana fama da matsalan halin hauka.
“Wani abu ne da ya zama ruwan dare a cikin sojoji. Amma wannan ba hujja ba ce ga kowane soja ya kasance yana tafka irin Wannan ta’asar.”