Sojojin Najeriya Sun Kama Jirgin Ruwa Cike Da Gangan Danyen Mai 600 Da Aka Sato A Delta.
Sojoji tare da hadin gwiwar jami’an tsaro mai suna Tantita Security Services sun damke wani jirgin ruwa a garin Warri na jihar Delta cike da sama da ganga 600 na danyen mai daga baragurbi.
Kamfanin dai wani mai ba da shawara ne kan harkokin tsaro da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya kulla domin kare kadarorin danyen mai a yankin Neja Delta.
Jirgin ruwan wanda ake zargin an yi amfani da shi wajen kai danyen mai zuwa jirgin, an yi amfani da shi ne mai nisan mil 20 daga gabar tekun Warri inda a ranar Asabar da ta gabata sojoji suka dage cewa za su lalata jirgin.
Yayin da ‘yan jarida suka nuna damuwa dangane da illar tarwatsewar jirgin ruwan, sojoji sun lalata jirgin.