A karshe Ɗan takarar APC Tinubu Ya yi wa duniya bayanin yanda ya mallaki dukiyarsa
Asiwaju Bola Tinubu ya wanke kan shi daga zargin da ake yi masa na mallakar kudi ta muguwar hanya.
‘Dan takarar shugaban kasan yace a duk Gwamnonin da suka shude, babu wanda aka yi ta bincike irinsa.
Tinubu yake cewa ba’a same shi da laifi ba domin da hannun jari da gadon gidaje ya tara dukiya a Duniya.
Asiwaju Bola Tinubu mai takarar zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar APC ya yi magana a game da silar arzikinsa a Duniya.
Asiwaju Bola Tinubu yayi wannan bayani ne a lokacin da BBC tayi hira da shi a garin Landan, kasar Ingila, bayan gabatar da jawabi a Chatham House.
‘Dan takarar shugaban kasar yace a duk tsofaffin Gwamnonin jihohi da aka yi, babu wanda aka tasa da bincike kamarsa, amma ba a gano laifinsa ba.
Da aka nemi Bola Tinubu ya yi bayanin yadda ya samu tulin dukiya, Daily Trust tace ‘dan takaran ya nuna siyasa ta sa ake yawan masa tambayar nan.
Tsohon Gwamnan na jihar Legas ya zargi abokan gaba da yi masa bakin-ciki da hassada, yace ya narka kudi ne a kasuwancin da suka kawo masa riba.
Shin su ba su son dukiya ne? Idan su ba makiyan dukiya ba ne, kasuwanci suna kawo riba. Na bada misali da Warren Buffet.
Yana daga cikin manyan masu kudin Amurka da Duniya. Ya fara da sayen hannun jari, ya gaji gidaje. Ina jawo kaya suyi daraja.
Ba na musanya dukiya ta, babu tsohon Gwamnan da aka yi shekaru takwas ana bincika iri na, har zuwa 2007 da na bar karagar mulki.
Har yau kuma ga ni nan, kuma ban taba karbar wani mukani a gwamnati ba.” – Bola Tinubu
Da aka bijiro da zargin cewa harajin da ake biya a Legas suna shigowa aljihunsa, The Cable ta rahoto Tinubu yana mai musanya batun da cewa hassada ce.
Tinubu yace IMF ta binciki kudin da ke shiga da fita a Legas, kuma babu hujjar da ke nuna yana cin dukiyar al’umma, yace hassadar ‘yan adawa ce kurum.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim