Tarayyar Afirka Ta Nuna Goyon Bayanta Ga Ƙasar Falasdinu.
Bin Muhammad
A karshen tarukan ta, kungiyar Tarayyar Afirka ta jaddada cikakken goyon bayanta ga al’ummar Palastinu a halaltacciyar gwagwarmayar da take yi da mamaya da mulkin mallaka na gwamnatin sahyoniyawan.
Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (AS) ya habarta cewa, a karshen zagaye na 36 na tarukansu a birnin Addis Ababa, shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka sun yi Allah wadai da ci gaba da adawa da gwamnatin sahyoniyawan da tsare-tsare da kuma bukatu da suka yi na neman sauyin Jagorancin Falasdinawa da al’ummar duniya don shiga cikin tattaunawar zaman lafiya.
Ita dai wannan kungiya ta jaddada goyon bayanta ga bukatar da Mahmud Abbas shugaban hukumar Palasdinawa ya gabatar ga babban sakataren MDD na samar da wani shiri na kasa da kasa na kawo karshen mamayar da gwamnatin sahyoniyawan take yi a yankunan Palasdinawa.
Ita dai wannan kungiya ta jaddada mahimmancin batun adalci na Falasdinu da kuma zaman lafiyarta tare da neman kasashe mambobin kungiyar da su ci gaba da goyon bayan al’amarin Palasdinu.
Shugabannin Tarayyar Afirka sun yi maraba da yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya tare da bukatar kotun Hague ta yanke hukunci kan mamayar da yahudawan sahyoniya suka yi wa yankunan Palasdinawa tare da jaddada goyon bayansu ga yunkurin Palasdinawa na neman zama mamba a Majalisar Dinkin Duniya.
Wannan kungiyar ta bukaci kasashe mambobinta da su mutunta matsayin birnin Kudus na tarihi.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta kira duk wani matakin da gwamnatin sahyoniyawan ta dauka a matsayin mara inganci tare da yin Allah wadai da ayyukan mulkin mallaka na wannan gwamnati da kuma manufofin kisa da tsare da kuma cin zarafin fursunonin Palasdinawa.
Ita dai wannan kungiya ta yi Allah wadai da cin zarafi da gwamnatin Sahayoniya ke ci gaba da yi a zirin Gaza tare da nuna damuwa kan tabarbarewar tattalin arziki da jin kai.