Uwargidan ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar All Progressives Congress APC, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce tikitin takarar musulmi da musulmi na jam’iyyar zai sanya wani sabon salo a fagen siyasar ƙasar nan bayan 2023.
Uwargidan Tinubu ta bayyana haka ne a ranar Larabar da ta gabata a yayin taron mata na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC na Kudu maso Yamma da aka gudanar a Mobolaji Johnson Arena da ke Legas.
Ta ce, “Game da tikitin tikitin musulmi da musulmi lokacine, wannan shi ne zai sa wani lokaci nan gaba, muma asami tikitin Kirista kaɗai. Abin da Allah ya yi a ƙasarmu yana da ban mamaki.
“Ina kawo muku gaisuwar ban girma daga uwargidan shugaban ƙasa, mai girma Aisha Buhari. Tare da miƙa soyayyarta da fatar alkairi ga ilahirin al’ummar garin Legas.
“Mun gode muku da kuka fito da yawa duk da ƙalubalen da ake fuskanta. Zuwa na nan wani dawowar gida ne. Kimanin shekaru 23 da suka gabata Allah ya albarkaci mijina ya zama gwamna, kuma a yanzu na mara masa baya a matsayin nazama matar shugaban ƙasa.
“Ina so in gode wa mutanen Legas ta tsakiya da suka aiko ni in wakilce su. Ni ce mace ta farko da ta zama Sanata sau uku. Wannan dama ce mai ban sha’awa, kuma na yi aiki don amfanin mutanenmu tun 2007 lokacin da mijina ya bar ofis.”
Ita ma da take jawabi a wajen taron, uwargidan gwamnan jihar Legas, Dakta Ibijoke Sanwo-Olu, ta yi kira ga matan jihar da su zaɓi jam’iyyar APC a zaɓen 2023 mai zuwa.
Ta ce a wani ɓangare, “Alƙawarin shugabancin Tinubu-Shettima shi ne cigaban ƙasa, kuma ‘yan Najeriya kada suyi la’akari da shekaru, launi, jinsi, ƙabila, addini, ko siyasa ba, za a tallafa musu don cimma burinsu da. Wannan shugaban ƙasa zai yi duk mai yiwuwa don ƙara wa mata dama a siyasa da yanke shawara.”
A nata jawabin, shugabar matan jam’iyyar APC ta ƙasa, Dokta Beta Edu, ta Buƙaci ‘yan ƙasar da su shirya katin zaɓe na dindindin, inda ta ƙara da cewa Tinubu zai ƙarfafa mata da samar da ayyukan yi ga matasa.
Tun da farko, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa jam’iyyar za ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Sanwo-Olu ya bayyana haka ne a yayin wata ziyarar ban girma da uwargidan Tinubu ta jagoranta a madadin babban uban ƙungiyar yaƙin neman zaɓen mata na Tinubu/Shettima.
RAHOTO:- Comrd Yusha’u Garba Shanga