Tinubu Ya Nada Sabbin Masu Bashi Shawara Na Mutane 8
Daga Al-Asad Al-Amin Funtua.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis ya amince da nadin masu ba da shawara na musamman guda takwas.
An bayyana nadin ne a wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis ta hannun Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin tarayya, Abiodun Oladunjoye.
Sanarwar ta bayyana cewa an nada Mista Dele Alake a matsayin mai ba da shawara na musamman, ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru; Malam Yau Darazo, mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa da gwamnatoci; Mista Wale Edun, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudi; da Mrs. Olu Verheijen, mai ba da shawara na musamman kan makamashi.
Sauran wadanda aka nada sun hada da Mista Zachaeus Adedeji, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga; Malam Nuhu Ribadu, mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro; Mista John Ugochukwu Uwajumogu, mai ba da shawara na musamman kan harkokin masana’antu, kasuwanci da zuba jari; da Dr Salma Ibrahim Anas, mai ba da shawara ta musamman kan harkokin kiwon lafiya.
Wannan na zuwa ne makonni bayan da Tinubu ya nada tsohon kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan sa (COS), yayin da aka nada George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya (SGF).