Tsohon gwamnan Jihar Adamawa Jibirila Bindow ya fice daga Jam’iyar APC.
Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow, ya yi murabus daga jam’iyyar APC.
Tsohon gwamnan ya bayyana dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar da rikicin jam’iyyar da bai warware ba.
Bindow ya ce rikicin jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa da bai warware ba ya sanya shi mika takardar ficewa daga jam’iyyar don haka ya daina zama dan jam’iyyar APC.
Murabus din da tsohon Gwamnan ya yi a ranar Laraba, ya janyo cece-ku-ce daga babban sakataren kungiyar APC na jihar Mustapha Ribadu.
Ribadu ya bayyana ficewar Bindow a matsayin babban rashi ga jam’iyyar APC a Adamawa.
A wata hira da ya yi da manema labarai a Yola ranar Laraba, Mustapha ya ce ci gaban babban koma baya ne ga jam’iyyar idan aka yi la’akari da irin dimbin goyon bayan da ake da shi da kuma fatan alherin da har yanzu tsohon gwamnan ke samu a jihar.
Wasikar murabus din Bindow mai dauke da kwanan watan Janairu 20, 2023, ya aike wa shugaban jam’iyyar APC a gundumarsa ta Kolere, karamar hukumar Mubi ta Arewa, ta nuna cewa tsohon gwamnan ya fice daga jam’iyyar ne bayan da aka shafe watanni ana rade-radin cewa zai fice daga jam’iyyar.
Bindow a cikin wasikar ya ce ya dauki matakin ne bayan “duka mai zurfi da tattaunawa da ‘yan uwa da masu ruwa da tsaki da kuma mabiya a ciki da wajen jihar Adamawa.”