Ƙungiyar Ƴan ta da ƙarin baya wato IPOB, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta bari yankin Igbo ya ɓalle tun da Arewa ta sami mahaƙa ɗanyen manfetur.
IPOB ta ce dama Arewa cima zaune ne kuma arziƙin man yankin Igbo ne suke kwaɗayi suka hana kafa Biyafara.”
Gwagwarmayar kafa ƙasar Biyafara ya fara ne tun shekarar 1967 inda aka yi yaƙin basasa lokacin mulkin Yakubu Gowon.
Ƙungiyar rajin kafa ƙasar Biyafara watau IPOB ta bayyana cewa tun da Arewa ta samu arzikin man fetur yanzu ya kamata a bari su ɓalle daga Najeriya.
IPOB ta bayyana hakan ne ranar Juma’a a jawabin da ta fitar cewa ai tuni dama arziƙin man feturin kudu da arewa ke amfana da shi yasa basu su son yankin Igbo su ɓalle daga kasar.
Kakakin kungiyar, Emma Powerful, wanda ya fitar da jawabin yace yanzu Allah ya amsa addu’ansu Arewa ta samu mai, suna fatan hakan zai gamsar da gwamnati ta barsu su fita daga Najeriya, rahoton ALFIJIR HAUSA.”
Zaku tuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya ƙaddamar da hakan arzikin man fetur karon farko a Arewacin Najeriya.
Tun Da An Samu Arziƙin Man Fetur a Arewa, A Bari Mu Fita Daga Najeriya, IPOB ta kara jaddadawa.”
IPOB ta ce duk arziƙin ma’adinan cikin ƙasa da Allah ya baiwa Arewa, yankin ya dogara kan arziƙin man feturin yankin Igbo ne.”
A cigaba da sanarwar, Yace, Arewacin Najeriya na da arziƙin man fetur da ma’adinai. Amma saboda su cima zaune ne, shirya suke su yi duk mai yiwuwa saboda arzimin man ƙasar Biyafara.”
“Yau, Allah ya daidaita matsalar ɗumbin shekaru tun da an samu mai a Arewa kuma hakan zai sulhunta gamayyar na dole su ɓalle daga Nijeriya.”
Babu ruwan al’ummar Biyafara da man ku. Abinda suke bukata shine zaman lafiya don yin kasuwancin su ba tare da yan ta’adda suna damun su ba.”
“Tun da kowa ya samu arziƙin mai yanzu, shin za’a bari kowa ya kama gabansa?”
Rahoto: Zuhair Ali Ibrahim.