Uba Sani Ya Dauki Aniyar Kudirin Biyawa Dalibai 1000 Kudin Jarabawar WAEC da NECO
A wannan wata da muke ciki dai-dai lokacin da ya rage kwanaki kadan sababbin Shugabanni su karbi rantsuwar kama Aiki wanda suka ha’da da Zababbun gwamnoni sanatoci ‘yan Majalisu da Shugaban Kasa Bincike ya nuna cewa a duk yankin Arewacin Nageriya mai dauke da jihohi goma Sha Tara mun Gano cewa Sanata Uba sani na kaduna Sanata Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijai Nageriya Kuma sabon Zababben gwamnan jihar Kaduna shine sabon gwamna Mafi Taimakon Al’umma da zai karbi rantsuwar shekarun farko na zama gwamna.
Sanata Uba sani wanda ya dauki nauyin kudrorin Ashirin da biyu a Majalisar dattijai a cikin kudrorin wasu tuni Shugaban Kasa Mohammadu Buhari ya sanya masu hannu zun zama doka.
Ya dauki nauyin daliban Yan Asalin jihar Kaduna ya biya masu Jarabawar NECO da WAEC sama da mutun dubu Daya.
Ta hanyar Rance mara ruwa Ya samar da jari gama matasan Nageriya sama da mutun dubu Sha biyu 12 banki NIRSEL mallakin babban Bankin Nageriya CBN ne ya samar da wannan tsari bayan Sanata Uba sani amatsayin Shugaban Kwamitin Inshora Bankuna da sauran Cibiyoyin ku’di sun kafa wannan tsari domin samun sauki ga Al’ummar Nageriya.
Ya samar da tallafi domin rage radadi ga Al’ummar wanda sama da mutun dubu bakwai ne suka anfana.
Sanata Uba sani shine Mafi karfin social Media a duk Yankin Arewacin Nageriya a yanzu haka domin Yana taimakon matasa Yan social media.
Sanata Uba sani ya taimaki Addinin Islama ta Hanyar Gina makarantu da Taimakon tallafin motoci domin karfafa Kalmar Allah a zukatan Al’umma.
Ya Gina babbar Cibiyar koyar da sana’o’i a rigasa duk domin kawo Hanyar dogaro da Kai a Yankin Arewacin Nageriya.