“Wani mahaifi mai suna Malam.Hadi, ɗan asalin garin Damari a ƙaramar hukumar Zariya, yayi ikirarin cewa matsayar ƴarsa mai suna Zahra’u ba ta amince da zaɓin da ya yi mata ba na auren wani mutum mai mata uku duk da ita na huɗu ba sai ya yafeta ga dangin mahaifiyarta har abada.”
“Zahra’u dai budurwace mai ƙarancin shekaru, kuma ƴar makaranta, ita kuma a nufinta ta auri ɗan birni, duba ga yadda a birnin aka haifeta, kuma anan ta girma ta yi karatunta na zamani dana boko, tsakaninta da ƙauyensu sai wani lamirn abu ya faru.”
“Ha wala yau dai daman mahaifin yarinyar ya kamama mahaifiyar ƴar nasa hayane a birnin Zariya, inda shi kuma yake zaune tare da matansa uku a wani ƙauye da ake kira da Damari, a nan birnin Zariya aka haifi Zahra’u, duba ga tasowar Zahra’u ɗin sai mahaifinta yayi mata miji a ƙauyensu.”
Mahaifiyar yarinyar mai suna Malama Aminatu, daman ba aure a tsakaninsu sun rabu tun da jimawa. Inda Rahoto ke cigaba da bayyana cewa ƴar nasu ta taso ne a hannun mahaifiyarta kama tun haihuwarta har girmanta, cinta, shanta.
Dangin uba wato malam. Hadi sun rattafa hannu a bisa ka atafaf sai anyi wannan auren na Zahra’u da kuma shi wannan ɗan ƙauyen, bayan ɗauki ba daɗi da akaita yi a tsakanin dangin mahaifiyarta dana uban kan samun Rashin fahimta na yuwuwar auren.
Hakan ya ƙara buɗe wani sabon fai-fai ne, inda Malam Hadi ya tabbatarwa duniya cewa, matsayar Zahra’u bata auri wannan ɗan kauyenba wanda ya zaɓammataba Tom zai yafeta ga dangin mahaifiyarta, kuma ya cireta daga sahun ƴaƴansa 25, da nufin taje can bairiki yayi mata aure duk inji shi.”
Rahoton na cigaba da cewa, hakanan dai Zahra’u ta amince da umarnin mahaifinta na zata auri wannan dan ƙauyen, duba da irin kalamin da ya furta na yafeta zuwa ga dangin mahaifiyarta, kuma koda aurenta ya tashi a can Birni baisantaba kuma kar a nemasu a matsayin dangin uba.”
Rahoto: Barrista Nuraddeen Isma’eel.