Daga Hajiya Mariya Azare.
“Wani uba ya lakawadawa saurayin ‘yar shi duka sakamakon ya hanashi kula ‘yar shi, uban ya gargaɗi saurayin kan cewa kada ya sake ganin shi a kofar gidan shi domin bai yadda da tarbiyan shiba saboda haka bazai iya bashi ‘yar sa ya aura ba.
Jaridan Alfijir tayi hira da ƙanwar mahaifiyan yarinyan “inda ta sheda mana cewa, saurayi da budurwan sun daɗe suna soyayya amma sam uban budurwan yaƙi yarda suyi aure, yahana ‘yar tashi fita ko makaranta saboda gudun haɗuwa da saurayin sannan ya hana saurayin zuwa ƙofan gidan shi amma yakiji.
Matan tace saurayin mai suna Baffah, yazo yana leƙa gidan su budurwan kamar yadda ya saba kwatsam saiga uban nan take ya hau dukan shi harsai da ya raunata shi, inda yanzu haka saurayin yake hannun ma’aikatan lafiya ana masa magani inda ita kuma budurwan kuma ta gudu daga gidan.
jami’an ‘yan sanda jihar bauchi sun kama uban suna bincike akan lamarin.