Daga Shamsu S Abbakar Mairiga.
Rundunar ƴan sandar jihar Kano, ta kama mai laifinnnan, wanda yayi garkuwa da ɗan shekara 5 mai suna “Hamza Harisu” kana ya kashe sa.
Mai laifin da farko ya buƙaci kuɗin fansa, na Naira miliyan ashirin 20,000,000. daga baya suka dai-dai ta a Naira miliyan biyan 5,000,000, kafin ya kashe yaron.
Mai magana da yamun rundunar ƴan sandar shelkwatar “Abdullahi Haruna Kiyawa” yace “a lokacin da baban yaron ya sanar da faruwar abun, sai shugaban rundunar ƴan sandar jihar Kano “Abubakar Lawal” ya haɗa runduna ta musamman daga “Bala Sha’aibu” ta shelkwatar ƴan sandar “Doguwa” domin a fuskanci lamarin”
“Da ƙoƙari na Musamman da ƙungiyar ƴan sandar ta yi, ta yi nasaran kama mai laifin mai suna “Ado Ibrahim” da ƴan uwan sa su 3 masu laifin. Dukan su daga ƙauyen “yantama” cikin ƙaramar hukumar “Doguwa” “Ado Ibrahim” ya amsa laifin cewa shi yayi garkuwa da yaron tun 27 Nuwamba shekara ta 2022. da karfe bakwai na yamma kana ya wuce da shi daji domin riƙesa”
ALFIJIR HAUSA, tattaro cewa, gidan wanda ya aika ta laifin, matasa sun ƙona ƙurmus.