Wani abun fashewa ya fashe a Sokoto, Wanda ya kai ga rasa ran Mutun hudu.
Wani abin fashewa da ya fashe a jihar Sokoto ya janyo asarar rayukan mutum huɗu, yayin da wasu da dama suka jikkata
Lamarin dai ya auku ne a shagon wani mai walda a cikin karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto a Arewacin Najeriya
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta kara da cewa mutanen da suka jikkata ana ba su kulawa a asibiti
Aƙalla mutum hudu sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata, bayan wani abin fashewa ya fashe a shagon wani mai walda a ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ransa ya firgita lokacin da ya ji karar fashewar abin, inda ya yi tunanin cewa yan bindiga ne suka kawo hari a garin.
“Lokacin da na ji karar fashewar, na yi zaton cewa yan bindiga ne suka kawo farmaki.”
“Sai a lokacin da na ga mutane sun ruga da gudu zuwa wajen shagon mai waldar inda lamarin ya auku sannan hankali na ya kwanta cewa ba yan bindiga ba ne suka kawo hari.”
“Bayan na yi bincike, an gaya min cewa fashewar ta auku ne a shagon wani mai walda, sannan an samu asarar rayuka yayin da wasu da dama suka raunata.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin kakakin rundunar yan sandan jihar Sokoto, DSP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da cewa lamarin ya auku ne ranar Lahadi da rana.
Kakakin rundunar yan sandan ya bayyana adadin waɗanda suka rasa ransu a matsayin mutum hudu.
“Fashewar ba ta da alaƙa da rashin tsaron da yankin ya ke fama da shi. Ta auku ne a dalilin fashewar tulun gas a shagon wani mai walda a yankin wanda ya janyo asarar rayukan mutum huɗu.
“Waɗanda suka samu raunika suna cikin mawuyacin hali, sannan ana kula da lafiyarsu a wani asibiti wanda ba a bayyana sunansa ba a yankin.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.