Wani Mai Gadin Banki Ya Zama Ma’aikacin Banki.
Daga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)
Wani jami’in tsaron banki ya je ya sami manajan bankin da ya ke aiki da ƙarfin hali ya shaidawa manajan cewa ya kammala karatunsa kuma zai so ya shiga jarrabawar cancantar neman muƙamin da za a yi a wannan lokacin.
Nan take shugaban bankin ya ba shi damar rubuta jarabawar, bayan rubuta jarabawar, a ƙarshe shi ne mafi kyawun ɗan takara kuma a ƙarshe ya sami wannan aikin.
Wannan hoton ya nuna shi a ranar juma’a tare da manajan bankin a matsayin mai ba da tsaro da kuma ranar litinin a matsayin ma’aikacin bankin da ya ke aiki a matsayin mai ba da tsaro.
Haƙiƙa, Allah ya na iya yin yadda ya so kuma ya canza yanayin ku, amma dole ne ku kasance a shirye, ku yi amfani da damar da ku ka samu idan sun zo. Kada ku ɗauki halin da ku ke ciki a matsayin makomarku ta ƙarshe.