Wani Mai Laifi Ya Fice Ta Tagar Kotu Ana Tsaka Da Gudanar Da Shari’a A Jihar Ondo.
Wani mutum mai suna Segun Akala, da ake tuhuma da laifin sata, ya tsallake tagar kotu kuma ya gudu bayan an ba da umarnin tsare shi a gidan yari
Sai dai ya yi rashin sa a, domin kuwa jami’an ‘yan sandan da ke harabar kotun, sun taimaka wajen cafko shi sannan kuma suka dawo da shi kotun.
Amma kuma sa a ɗaya da ya yi ita ce, kotun ta amince da bayar da belinsa bisa tara ta kuɗi da kuma wasu sharuɗa da ta gindaya masa
An dan samu wata ‘yar karamar dirama a kotun majistare da ke Odigbo, hedikwatar karamar hukumar Odigbo ta jihar Ondo, yayin da wani da ake kara mai suna Segun Akala ya fece daga kotun bayan da alkalin kotun ya bayar da umarnin tsare shi.
The Punch ta tattaro cewa an kawo Akala gaban kotun ne bisa zargin sata, kuma an gurfanar da shi ne gabanta kan tuhumar hakan.
Wata majiya a kotun ta ce, alkalin kotun, D. O Ogunfuyi, ya ba da umarnin tsare wanda ake kara, Segun Akala.
Da jin wannan umarni na kotun ne wanda ake karar ya haura ta tagar kotun, sannan ya tsere zuwa cikin jeji duk da cewa akwai mari (handcuff) a hannunsa.
Majiyar ta kara da cewa sai dai taimakon ‘yan sanda da ke harabar kotun ta yi nasarar cafko mai laifin.
Ana zargin wanda ake tuhumar ne da satar sarkar injin yankan itace da kuma kayan sawa da kudinsu ya kai N336,000, mallakin wani mai suna Akintan Akintade.
Tun da farko, jami’in da ya shigar da kara, Usifo James, ya sanar da kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Mayun 2023 a titin Aipon, da ke Odigbo, jihar Ondo.
A cewar mai gabatar da karar, laifin da aka aikata ya sabawa sashe na 390 (9), na kundin laifuffuka na shekarar 200, na jihar ta Ondo.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi.
Lauyan mai gabatar da kara ya nemi a dage shari’ar domin ya samu damar yin nazari a kan fayil din karar da kuma shirya shaidunsa, sai dai lauyan wanda ake kara, Mista Rufus Omotayo ya roki kotun da ta bayar da belin wanda ake karar.
Babban Alƙalin kotun, Ogunfuyi, a hukuncin da ya yanke, ya bayar da belin wanda ake ƙara a kan kudi N100,000 tare da sharaɗin kawo mutane biyu da za su tsaya masa, kamar yadda Naija News ta kawo.
Ya ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan yari na Okitipupa, har zuwa lokacin da sharadin belin nasa ya cika, sannan ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2023.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim