Wani Makaho A Najeriya Ya Nemi Auren Tsaleliyar Budurwa.
Wata kyakkyawar budurwa ta gaza yarda da abun da idanunta suka gani yayin da amininta mai lalurar makanta ya nemi ya aure ta a kasuwa.
Ya zo da abokinsa da kuma wani shahararren dan TikTok don ayyana kudirinsa amma dai abun bai yi wa budurwar dadi ba sosai.
Bayan ta tsere daga shagonta da farko, matashiyar ta sake dawowa wajen don amincewa da bukatarsa cikin yanayi mai tsuma zuciya
Wani dan Nijeriya mai lalurar makanta ya haddasa cece-kuke a kasuwa yayin da ya nemi auren aminiyarsa cikin yanayi na bazata.
Obinna ya ce ya san Juliet kafin ya makance kuma cewa sun shafe tsawon shekaru biyar suna abota.
Lokacin da ta shiga matsalar rashin muhallin zama, shi da kansa ya bukaci ta dawo gidansa da zama inda ita kuma ta dungi kula da shi.
Bayan ya tuntubi shahrarren dan TikTok Theo Ayomoh, Obinna da abokinsa Hemes sun fito don ba Juliet mamaki a kasuwa inda take aiki.
Da zuwansu wajen, Obinna ya yi godiya ga Juliet kan kasancewarta aminiya tagari sannan ya bijiro mata da maganar aure.
A bidiyon TikTok din, Juliet ta gudu ta bar shagonta yayin da ta samu labarin cikin kaduwa. Ta fadama Theo cewa bata so yadda bai sanar da ita ba kafin zuwan abun.
Bayan dan lallashi, ta dawo don karbar zoben Obinna, lamarin da ya yi wa mutane dadi.
Jama’a sun yi martani
@Adebayo poush ya ce:
“Wasu lokutan mata mafi alkhairi gareku ba lallai ya zo a yanayin abun da kuke so ba amma kada ku kori ni’ima da mijinku saboda yanayin yadda yake.”
@Alexi Atanga ya ce:
“Allah Ubangiji ya ci gaba da tallafa maku sannan ya baku kyawawan yara, ya kamata duniya ta tallafa masu.”
@Emma Juliet276 ta ce:
“Juliet Allah ya yi maki albarka saboda wannan farin cikin, Allah ka taimaka ka dawo masa da ganinsa.”
@fauziatagoe842 ta ce:
“Na yi kuka Allah ya saukaka radadin duk wata zuciya da ke shan wahala a fakaice sannan ya yi maki albarka yar’uwata ya kuma kareku.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.