Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Enugu da ke sashin binciken kisan gilla na sashen binciken manyan laifuka na jihar CID Enugu, tare da takwaransu na rundunar ƴan sandan jihar Imo, sun kama wani Osuagwu Chidubem (namiji) a Nekede Owerri, jihar Imo a lokacin da yake yunƙurin siyar da wata mota kirar Toyota Corolla. Da ya yi awon gaba da ita a hannun babbar masoyinsa, wata Amarachi Chukwu mai shekaru 32, bayan ya kashe ta.
Wanda ake zargin, a cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan Enugu (PPRO), Daniel Ndukwe, ya aikata laifin ne a ranar 01/11/2022 a gidan marigayan da ke Meniru, Awkunanaw, Enugu.
“Bincike ya nuna cewa, wanda ake zargin da ƴan tawagarsa gaba ɗaya, sun haɗa baki ne da safiyar ranar da aka ambata, inda suka je gidan wadda aka kashen, suka yi yunkurin kwace mata key ɗin Toyota Corolla, wanda ta bijire. Kuma a kan tsayin daka, suka ɗaure hannayenta, kafafu da bakinta da tufafi; ya kulle ta a cikin gidan sannan suka tafi da motar,” in ji ƴan sanda.
Sanarwar ta kara da cewa: “Sai dai an gano gawar ta a gidan da aka ce a ranar 04/11/2022, bayan da jami’an ƴan sanda da ke aiki a sashin ƴan sanda na Ikirike na rundunar suka buɗe kofar da karfi, bayan samun rahoton cewa wani wari mai ban haushi yana fita daga falon.
“Jami’an ƴan sanda sun ɗauki gawar zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar ta, sannan aka ajiye gawar a ɗakin ajiyar gawa domin adanawa da kuma tantance gawar.
“Saboda haka an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike kuma an tsare shi a gidan kurkuku har sai an ci gaba da sauraron karar.”
Rahoto Shamsu S Abbakar Mairiga.