Wani Matashi Mahayin Doki Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Dattijo Dan Shekaru 70
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar dattijon da wani mahayin doki ya buge a karamar hukumar Ringim
Mahayin dokin mai suna Muhammad Mustapha mai shekaru 25 ya buge dattijon ne mai shekaru 70 akan kekensa a unguwar Maina
Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar dattijon a babban asibitin Ringim tare da tsare mahayin dokin a ofishinsu
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani dattijo dan shekara 70 bayan wani mahayin doki ya buge shi.
A ranar Asabar ne 10 ga watan Yuni wani matashi mahayin dokin ya buge dattijon a unguwar Maina cikin karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawal Jiisu ne ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi 11 ga watan Yuni na wannan shekara.
Ya ce a ranar Asabar 10 ga watan Yuni, wani mahayin doki mai suna Muhammad Mustapha mai shekaru 25 ya gagara shawo kan dokin da yake kai tare da buge wani dattijo mai keke a cikin unguwar Maina.
Dattijon mai shekaru 70 mai suna Umar Hassan da ke unguwar Galadanci an buge shi ne akan kekensa inda ya samu raunuka da dama da kuma karaya a kafarsa ta hagu da kuma kafadarsa.
Ya kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun isa wurin da abin ya faru tare da daukan marar lafiyar zuwa babban asibitin Ringim, kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro.
Jiisu ya tabbatar da cewa dattijon daga baya ya rasa rayuwarsa a asibitin bayan an fara ba shi kulawa na musamman.
Ripples Nigeria ta tattaro cewa, jami’an ‘yan sandan sun mika gawar mamacin ga ‘yan uwansa don shirye-shiryen binnewa yayin da hukumar ke ci gaba da tsare mahayin dokin.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim