Wani matashi mai suna Babe Face ya kashe budurwarsa tare da ƙona kanshi a Jihar ribas
A cewar wani ganau, wanda ya zanta da ALFIJIR HAUSA, Babe Face ya kan gayyaci masoyinsa zuwa gidansa a duk ƙarshen mako.
Shaidan ya ce rikicin ya fara ne a lokacin da Suka Samu ɗan rashin jituwa a tsakaninsu a Cikin gidan.
A ƙoƙarin da yake yi na rufe hanyarsa, Babe Face ya cinnawa gidan wuta kuma ya ƙone ƙurmus tare da gawar budurwar tasa.
“Lamarin ya farune a ƙarshen mako a yankin Kom Kom na Oyigbo. Wani matashi mai suna Babe Face ya samu sabani da budurwar sa kan batutuwan da suka shafi yaudarar da ta yi masa a cikin dangantakarsu,” inji majiyar.
“Ya yi wa marigayiyar dukan tsiya kuma ya shaƙeta a cikin lamarin. Bayan da ya samu nasarar kashe yarinyar, yaron ya kona gidansa a wani yunkuri na rufe hanyarsa amma wutar ta kama shi har lahira tare da gawar masoyinta.”
Majiyar ta kara da cewa; Kamar yadda ALFIJIR HAUSA ta bi lamarin ya haifar da firgici a yankin, yayin da mazauna unguwar suka fice daga yankin saboda fargabar kama su daga hannun ‘yan sanda.