Wani Matashi Ya Aje Aikin Sa Domin Faranta Ran Budurwarsa Sai Dai Bayan Sati Biyu Ta Rabu Da Shi
Wani matashi ya ajiye aikinsa a kamfanin man fetur domin ya kasance tare da budurwarsa wacce ke zaune a wani birnin daban, basu daɗe ba suka rabu
Ya sanya labarinsa ne a Twitter inda ya yi amfani da #LoveMadeMeDolt, wanda ya yaɗu sosai a manhajar Twitter
Mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu akan labarin nasa, inda wasu suka tausaya masa yayin da wasu suka caccake shi
So makaho ne wanda baya ji baya gani kuma ya kan sanya mutum ya yi wani abu wanda hankali ba zai ɗauka ba.
Hakan shi ne abinda ya faru da wani matashi wanda ya ajiye aikinsa a wani kamfanin man fetur mai girma a Port Harcourt, domin ya kasance da budurwarsa wacce take a birnin Ibadan.
Matashin wanda yake amfani da sunan @Phoenix23 a Twitter, ya sanya labarinsa ne a kafar ta sada zumunta.
Ya bayyana cewa ya yi murabus daga aikin da yake yi mai gwabi a kamfaninman fetur din, saboda yana son ya kasance kusa da budurwarsa wacce ke zaune a wani garin daban.
Ya yi fatan cewa idan ya koma Ibadan, za su samu isashshen lokacin da za su raini soyayyarsu ta yi kwari sosai.
Sai dai, abubuwa ba su tafi masa yadda ya tsara su ba. Ya bayyana cewa sun rabu bayan sati biyu kacal da komawarsa Ibadan.
Bai bayyana dalilin da ya sanya suka rabu ba, amma ya yi dana sanin wautar da ya yi ta barin aikinsa.
Matashin ya bayyana cewa ya san ya yi sakarci wajen barin aikinsa saboda soyayya sannan ya bukaci mutane da kada su yi masa hukunci kan kuskuren da ya aikata.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim