Wani Matashin Dan Banga Ya Bindige Abokin Takararsa Saboda ya Kwace Masa Budurwa
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas na gudanar da bincike kan lamarin da wani dan banga ya bindige wani mutum har lahira saboda ya yi wa budurwarsa magana
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Nnwonyi Emeka ya gargadi ‘yan bangan kan wuce gona da iri da suke yi da kuma take hakkin bil’adama da wata kungiyar ‘yan bangan ke yi
Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Victor Erivwede, ya bayyana cewa ‘yan kungiyar banga ta OSPAC, na da hannu wajen aikata miyagun laifuka da dama a jihar
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta ce tana gudanar da bincike kan wani lamari da wani dan banga ya bindige wani mutum saboda zargin kula budurwarsa da yake yi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Nwonyi Emeka, a zantawarsa da manema labarai a Fatakwal, ya yi gargadi kan yawaitar ‘yan banga a jihar, saboda mafi yawa daga yan bangan wata kungiyar banga OSPAC, duk masu laifi ne a wurin jami’an tsaro.
Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan, Victor Erivwede, wanda shi ne mai kula da sashen binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar, SCIID, ya ce ana yawan samun laifin cin zarafin bil’adama da kungiyar ‘yan bangan ke yi.
Ya ce da farko ‘yan bangan na OSPAC suna yin abin da ya kamata, amma daga lokacin da suka fara karbar aikin ‘yan siyasa, sai suka baude suka kama aikata laifuka, kamar yadda Vanguardta wallafa.
Victor ya kara da cewa, da ace yana da iko, da lallai zai bai wa kwamishina shawarar a kara duba yanayin yadda suke gudanar da aiki.
Ya ce mafi yawansu ana yawan kawo kararsu kan yawan samunsu da ake yi da aikata miyagun laifuka.
A cewarsa yawancin ‘yan OSPAC masu laifi ne. Ina da wata shari’a a gabana, inda wani dan banga ya harbe wani mutum har lahira saboda wai ya yi magana da budurwarsa.”
A nasa bangaren, kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Ribas, Emeka, ya ce duk da cewa ‘yan bangan suna da amfani, hakan ba yana nufin za su zura musu ido suna cin karensu babu babbaka ba.
Kwamishinan ya ce: ba za mu yarda da yanke hukunci da ‘yan bangan ke yi ba. Ba za ta yiwu ace masu kare rayuka da dukiyoyin jama’a, su ne kuma ke bi suna kashe mutane. Dole ne mu dakile wannan zaluncin da ’yan bangan ke yi.”
Ya kuma bayyana cewa, ‘yan bangan ba jami’an tsaro ba ne, inda ya ce an taba samun lokacin da suka koma masu karbowa mutane basussuka, wanda suka rika gallazawa mutane a dalilin hakan.
Kwamishinan ya kara da cewa aikin ‘yan bangan shi ne su kama wanda ake tuhuma da laifi da kuma musayar bayanai tsakaninsu da jami’an tsaro.
Da yake zantawa da shugabannin ‘yan banga na jihar, kwamishinan ya ce ba ku da ikon tsarewa ko yin bincike. Idan kotu ta yankewa wani hukuncin kisa ta hanyar rataya, sai aka samu wani ya harbe shi, to wannan da ya yi harbin ya aikata laifin kisa.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim