Wani mutum ya Jefa Mahaifinsa a cikin rijiya.
Wani dattijo mai shekaru 60 da haihuwa yana gwagwarmaya don ceto rayuwarsa a asibitin gundumar Longisa bayan ya shafe kwanaki uku a cikin rijiya mai tsawon ƙafa 20 da ɗansa ya jefa shi a ciki.
Ɗan sa mai suna Samuel Tanui ya jefa shi cikin rijiyar sakamakon rikicin filaye, a yankin Emitiot da ke yankin Chepalungu a gundumar Bomet a ƙasar Kenya.
A cewar mataimakin shugaban yankin Cif Lenny Ngeno, tun da farko Tanui ya ƙi bai wa ɗansa mai shekaru 22 Charles Kiplangat Rotich izinin sayar da fili ga iyalan kuma ana kyautata zaton hakan ne ya sa ɗan nasa ya kitsa wani shiri na kashe shi.
Bayan jefa shi cikin rijiya, Rotich ya ci gaba da harkokinsa na yau da kullum yana tunanin mahaifinsa ya rasu.
Dattijon ya yi nasarar kama ihu da kuka sosai don masu wucewa su ji, har akaci karo da masu gittawar sukaji aka ceto shi. Daga nan aka garzaya da shi asibiti.
RAHOTO:– Comrade Yusha’u Garba Shanga.