Wassanin Da Shagulgulan 12 za’a gabatar domin Mika Mulki Har Na tsawon Kwanaki 7.
An shirya taro da liyafa da bukukuwa dabam-dabam a shirye-shiryen rantsar da shugaban kasa
Boss Mustapha ya sanar da abubuwan da aka yi tanadi kafin Muhammadu Buhari ya mika mulki
Za a yi wadannan taro ne a Aso Rock, Masallacin kasa, Coci, Farfajiyar Eagle da sauran wurare
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya ce akwai taro da liyafa da lacca da za a gabatar duk a cikin shirye-shiryen rantsar da shugaban kasa.
Premium Times ta ce za a dauki mako guda ana shagulgula a birnin Abuja.
Zababbun shugabanni su na samun mafi girmar lambar yabo, a 2010 ne aka saba ka’ida da Goodluck Jonathan ya hau mulki, za ayi irin haka a wannan karo.
Dr. Goodluck Jonathan ya samu mulki ne bayan rasuwar Ummaru Yar’Adua, sai majalisar koli ta ba shi lambar yabon da ya zama sabon shugaban Najeriya.
A Ranar talata 23 ga watan Mayu 2023
liyafar da za a shirya domin karrama Shugaban kasa a gidan sojoji da karfe 7:00 na dare a ranar laraba 24 ga watan Mayu 2023.w
Taron majalisar FEC na karon karshe a dakin taron majalisar a fadar shugaban kasa ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu 2023.
Za a Karrama zababben shugaban kasa da mataimakinsa da lambobin girman GCFR da GCON da kuma mika takardun karbar gwamnati
A babban dakin taro na fadar shugaban kasa da karfe 10:00 na safe Mahalarta za su zauna da karfe 9:00ns
Ranar Juma’a, 26 ga watan Mayu 2023 za ai Lacca ta musamman da sallar Juma’a a babban masallaci da karfe 10:00ns da 1:30nr
Lacca din za a yi ta ne domin karfafa damukaradiyya wanda Mai girma tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru M. Kenyatta zai gabatar a babban dakin taro na kasa da karfe 10:00ns
Asabar 27 ga watan Mayu 2023 taron ranar yara za a gabatar da Fareti Liyafar yara a tsohon filin farteti da karfe 10:00ns a dakin taron fadar shugaban kasa da karfe 2:00nr
Ranar Lahadi 28 ga watan Mayu 2023 za ai zaman coci a babban cocin kasa da karfe10:00ns liyafar rantsuwa.
Ranar Litinin 29 ga watan Mayu 2023 faretin rantsuwa/mika mulki a farfajiyar Eagle Square, CBD da karfe10:00ns
Bayan rantsuwa fadar shugaban kasa da karfe 1:30 (za a shiryawa shugaban kasa, takwarorinsa da sauran shugabanni da wadanda aka gayyata).
Kafin Muhammadu Buhari ya mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, an ji labarin zai bada lambar yabo ga zababben shugaban kasa da mataimakinsa.
Baya ga lambar yabo na GCFR da GCON da Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima za su samu, Premium Times ta ce akwai abubuwa iri-iri da za ayi.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.