Babban Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya bayyana cewa wasu ƴan matan makarantar Chibok da aka ceto sun samu hanyar haɗuwa da wadanda suka sace su.
IGP ɗin ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata yayin wani taron tattaunawa na mako-mako da ƙungiyar kafafen yaɗa labarai na fadar shugaban ƙasa ta shirya a Abuja, inda ya bayyana cewa jami’an tsaron da ke magance tashe-tashen hankula a wasu lokutan kan zama dole su yi ƙasa a gwiwa da ƴan fashi ko masu garkuwa da mutane domin kuɓutar da waɗanda ake tsare da su ba tare da an samu matsala ba.
Ya ce, “Batun ƴan matan Chibok; ka san suna fitowa ɗaya bayan ɗaya kuma a hankali. Wani lokaci su fito su ce eh, mun zo ganin iyayenmu kuma muna son komawa.
“Don haka watakila an kama su ko kuma an san su da lamarin kuma an cusa su kuma sun kasance cikin waɗanda suka sace su.
Amma kamar yadda nake cewa, koƙari ne na cigaba, har ma a watan da ya gabata, ka ga wata ƴar Chibok ta fito da ƴaƴa biyu ko uku, ta ce ta zo gaishe da iyayenta ne kawai, kuma tana son komawa. Don haka, har yanzu muna kan haka, akwai fata.”
Hakan ya matuƙar ɗimautar da al’umma ganin cewa, Ƴan matan da aka ceto su daga hannun Boko Haram ɗin suna da burin su koma hannunsu domin cigaba da rayuwa.”
Bugu da ƙari akwai wasu matan da suke hannun Boko Haram ɗin waɗanda har sunyi aure da mayaƙan, inda kuma suka Bayyana tabbas suna jin daɗin zama mazajensu na su Ƴan Boko Haram ɗin, kamar yadda suke ƙoƙarin bayyana hakan ga jami’an tsaro mafi kusa.”
IGP ya nuna alhininsa matuƙa na ganin yadda ake ƙoƙarin ceto Ƴan matan na Chibok amma su kullum burinsu shine abar su; su cigaba da rayuwa da Ƴan Boko Haram ɗin a can daji ko kuma ace matsuginsu.”
Daga Shamsu S Abubakar Mairiga.