Babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasar Nigeriya Lucky Irabor, a ranar Alhamis, ya bayyana cewa ƴan siyasa na matsawa rundunar sojin ƙasar lamba domin yin sulhu a babban zaɓen shekarar 2023.
Ya kuma tabbatar wa ƙasar da cewa sojoji za su ci gaba da kasancewa ba tare da siyasa ba, yana mai kira ga jama’a da su ci gaba da amincewa da sojoji.
Mista Irabor, da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce galibi ana tursasa sojoji da hafsoshi da kuma matsa musu lamba wajen yin tasiri a zaben.
Sai dai ya ce jami’an za su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da sahihin zaɓe yayin da ake kokarin tabbatar da cewa ma’aikatan sun yi biyayya ga umarnin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na nuna ɓacin rai.
Ya kara da cewa an miƙa ka’idojin aiki kafin zaɓe da lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓen ga jami’an.
Ƴan Najeriya za su kaɗa kuri’a a watan Fabrairu da Maris na shekara mai zuwa domin zaɓen sabbin shugabanni a matakin jihohi da na tarayya. Ƴan takara 18 ne ke fafatawa domin maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zai kammala wa’adinsa na biyu a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Rahoto Shamsu S Abbakar Mairiga.