Wasu Ma’aurata Waddanni Sun Ba Hammata Iska
An hago wasu wadannin ma’aurata a lokacin da suke ba hammata iska
Matar, wacce alamu ke nuna tana da ciki ta gargadi mijin nata a lokacin da suke fada kana ta ture shi a gefe
Ganin yadda ta dawo daidai a lokacin da ta fadi a kasa, mutane da yawa sun shiga mamaki, sun bayyana ra’ayoyinsu
Wata mata mai karamin jiki da ta ragargaji mijinta a lokacin da suka barke da fada a cikin gida, fadan da ya ba mutane da yawa mamaki.
A wani bidiyon da ya yi shuhura a kafar sada zumunta, mata da mijin, wadanda duk wadanni ne sun yi fada mai ban dariya.
Da fari ture mijin nata ta yi a kasa, kana ta naushe shi a baya kamar wacce ke fada da sa’anta; amma ta fadi kasa.
Yayin da mijin ke kan gwiwarsa daya, nan da nan ita kuwa ta tashi ba tare da dafa kasa ba, lamarin da ya ba mutane mamaki.
Daga nan, matar ta kama kugu tana kuma tsayuwar fada kamar wacce ta yi damara kana ta fice daga wurin da mijin ke tsaye. Mutane da yawa a kafar zumunta sun yi mamaki.
Martanin jama’a
@Clementscalar cewa yayi Mutanen nan suna da kira ta daban kalli yadda ta tashi ba tare da dafa komai ba.
@ola_bukun ya ce Omo! Allah mai halitta kalli yadda ta tashi ba tare da rike komai ba.”
@stevewest223456: ta ƙara da Tambayata anan ita ce na ga tana da juna biyu amma bata da nono. Ta yaya za ta shayar da jajirinta?”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim