Wata Babbar Kotu Ta Daure Wani Likita Bayan Samun Sa Da Sakaci A Aikinsa
Wata babbar kotu a jihar Legas ta yanke hukuncin daurin shekara daya a gidan yari ga shugaban asibitin Excel Medical, Dakta Ejike Ferdinand Orji, bisa samunsa da laifin sakaci da kuma jefa rayuwar wani mara lafiya mai shekaru 16 cikin hadari.
Mai shari’a Adedayo Akintoye ya samu likitan ne a kan tuhume-tuhume 4 daga cikin shida da ake tuhumarsa da su.
A tuhumar da gwamnatin jihar ta shigar, an fara gurfanar da Dr Orji ne tare da matarsa, Dokta Ifeayinwa Grace Orji.
Wadanda ake tuhumar sun yi wata aika aika, a watan Yulin 2018, a cibiyar su ta kula da lafiyarsu, inda suka yi sakaci da rikon sakainar kashi lokacin da suka gyara wani rauni a kafar hagu na karamin yaro, wanda ya jawo masa mummunar illa.
Karamin matashin dan Najeriya mai burin buga kwallon kwando a kasar Amurka, ya gamu da ajalinsa sakamakon lamarin da ya faru a lokacin da ya zo Najeriya hutu.
A hukuncin da ta yanke, Alkalin ta sallami Dakta Misis Orji tare da wanke ta biyo bayan bukatar da Darakta mai gabatar da kara na jihar ta gabatar wanda ya dakatar da karar da ake mata.
Mai shari’a Akintoye ya ci gaba da cewa, Orji bai samu amincewar mahaifiyar mara lafiyar ba, wadda ke kwance a asibiti a lokacin da aka yi aikin din.
Lauyan wanda ake kara, Ajibola Ariba, a cikin karar da ya shigar, ya bukaci kotun da ta yi adalci da jin kai, tare da bayyana cewa wanda ake tuhuma shi ne mai laifi na farko wanda ba a taba yanke masa hukunci ba a baya, ya kuma roki kotun da ta duba zabin bayar da tara kamar duba da wanda ake karar ya na fama da shekaru.
Bayan roko nasa, Mai shari’a Akintoye ya ce, “Na saurari rokon a yi masa sassauci a madadin wanda ake kara. Don haka, wanda ake karar, Dokta Ejike Ferdinand, an yanke masa hukuncin daurin shekara daya kan kowanne, bisa laifuka biyu, uku, hudu, da shida.”