Wata Budurwa Da Ta Durfafi Coci Da Nufin Samo Miji Ko Ta Wani Irin Hali
Wata budurwa ta ce ko ta wane irin hali ne, dole ne ta sami mijin aure da take ganin ya dace da ita
A cikin wani faifan bidiyo da @ninacharles8 ta wallafa, ta nuna yadda ta shiga coci, ta na mai shan alwashin samun miji
Bidiyon ya haifar da muhawara a tsakanin mabiyanta a kan TikTok bayan wallafa shi, kuma ya yi ta yawo a dandalin
Wata budurwa da ta daura damarar neman mijin aure ta kutsa kai cikin wani coci domin neman wanda zai aureta.
A cikin wani faifan bidiyo da @ninacharles8 ta wallafa, budurwar ta ɗauki bidiyon kanta a yayin da take shiga cocin.
Ta ce ta na fatan samun mijin da ya dace da ita a cocin, inda ta sha alwashin cewa babu abin da zai dakatar da ita.
A cewarta, dole ne ta samowa kanta miji a cikin cocin, koda ta karfi da yaji ne.
Ta yi wa cocin tsinke da azama a muryarta a yayin da kuma ta ke bayyanawa mabiyanta na TikTok manufarta cikin daga murya.
Ta ce shugabannin addini sun fuskanci barazana a baya, sai da suka sa karfi sannan suka iya tabbatuwa, don haka ita ma za ta yi amfani da karfin wajen neman mijin nata.
Tsokaci daga masu amfani da TikTok yayin da wata budurwa ta durfafi coci domin neman mijin aure
@user9471732153921 prince ya ce:
“kwantar da hankalin ki, ga ni nan.”
@dasmithcomedy ya ce:
“Abinda kawai ya rage shi ne ki sanya sambol a gefen titi na neman mijin.”
@Fatokun Osuolale Olanrewaju ya ce:
“Sarauniyar zuciya.”
@babs Kuffay said:
“Ubangiji ya cika miki burin zuciyarki. Amin.”
@Johnson Ibe ya ce:
“Yi kokarin nemo mijin aure, ina miki fatan alkhairi.”
@King David ya ce:
“Da wasa kike? ta yaya hakan ta faru?”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim