‘Yan sanda sun kama wata malamar makaranta bisa zargin yi wa wata daliba ‘yar shekara hudu fyade a jihar Borno.
Malamar mai suna Aunty Zara da ke aiki da makarantar Golden Olive da ke Maiduguri babban birnin jihar, an ce ‘yan sanda sun kama malamar a makon jiya.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, Sani Kamilu, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ya ce mahaifin wanda ya shafa ne ya kai karar ga ‘yan sanda, inda ya kara da cewa an fara gudanar da bincike kan lamarin.
Hassan Dala, mahaifin wanda abun ya shafa, ya ce ya kai karar ga ‘yan sanda lokacin da ya lura fitsarin ‘yarsa ja ne.
“Da farko, na ɗauka alama ce ta kamuwa da cuta. Na kai ta asibiti, suka gaya mana mene ne matsalar,” in ji Dala.
“Lokacin da mahaifiyar ta tambaye ta, ta gaya mana abin da malamar ta yi mata.
Yarinyar ta ce malamar ta rungume ta, ta ba nononta ta tsotse, sannan ta sanya yatsa a cikin al’aurarta.”
Rahoto Kamal Aliyu Sabongida.