Wata mata a legos ta kashe kawar ta a yayin wani Zazzafan Musu a tsakanin su.
Wata mata mai suna Annie Ofili, tayi kokarin kashe kawar ta mai suna Glory Okon, har lahira.
A mazaunin ta dake Estate na Greenville, Badore a karamar hukumar Ajah dake jihar lagos.
Manema labarai sun samu rahoton cewa, a ranar da lamarin ya faru, Okon ta kaima Ofili ziyara a gidan ta.
A yayin da su duka biyun suke tattaunawa akan wani mai laifi da ake zargi a layin, Sai suka fara musu tsakaninsu, inda musun ya zama fada.
Mun samu rahoton cewa, a yayin musun tsakanin su, Ofili taje ta dauki wuka cikin kicin,
Wacce da itane tayi amfani ta daba ma kawar tata a wuya.
Dalilin da yasa a yayin musun aka samu wannan lamarin kenan, Wanda yayi sanadiyyar mutuwar Okon.
Wadanda suke kusa da su, sunce basu san lokacin da abun ya faru ba, kuma basu San dalilin faruwar hakan ba, Sun kara da cewa, sunji dai lokacin da suke hayaniya suna daga murya ga junan su.
Lokacin da akayi kokari bude kofar gidan domin a raba su, sai aka tarar da wannan aika aikar.
Majiya mai tushe tace, wani makwabcensu dake a gidan yayi ita baking kokarinsa domin ya bude kofar.
Sun kara da cewa, lokacin da aka bude gidan an samu Aika aikar da Ofili tayi, sun ga cewa, ta yima Okon rauni a wuya da baya.
Sun ce, a lokacin da muka bude muka shiga, sai muka samu Ofili ta haye bisa kawar ta Okon da wuka, kawar tata duk jini ya cika ta da kuma wukar.
Majiya mai karfi tace, anyi saurin tafiya da ita asibiti ta CMS dake Lagos, amma suna isa asibitin likita ya tabbatar da mutuwar ta.
Daga Rafi’atu Mustapha Katsina