Wata Mata Da Mijinta Ya Dauki Nauyin Karatunta Zuwa Birtaniya Ta Ce Ba Ta Son Mijin Nata.
Wata ma’aikaciyar jinya ta nemi shawarar masu amfani da kafafen intanet dangane da yadda ta ji ta daina son mijinta
Ta ce babu gaira babu dalili ta ji ta daina sonsa duk da shi ya dauki nauyin karatunta zuwa Birtaniya da ya ke da zama
Ta ce mijin ya magance ma ta matsalolinta da na ‘yan uwanta a lokacin da suke a Najeriya, sannan shine ya yi mata kokarin barin kasa
Auren wasu ‘yan Najeriya mazauna kasar waje na fuskantar kalubale biyo bayan bayanin da matar ta yi na cewar ba ta sha’awar auren yanzu.
Wata mai suna Anthonia Ogbewe ce ta wallafa labarin a shafinta na TikTok in da ta bayyana cewa matar na da shekaru 28 a yayin da mijin kuma ya ke da shekaru 32.
Matar ta ce mijin nata ne ya ce ta karanci ilmin jinya a sa’ilin da ta ke a Najeriya kuma shine ya rika taimaka ma ta wajen daukar nauyin karatun.
Matar ta kuma kara da cewar ya biya ma ta bukatunta da dama hadda ma wasu daga cikin bukatun ‘yan uwanta, sannan kuma shine ya dauki nauyin takardun tafiyarta zuwa kasar waje.
Ta ce ta fada masa cewa ita fa ba ta ra’ayin auren na su, amma kuma sai ya ke tunanin ko domin kawo ta kasar Turai da ya yi ne, kuma ya ke fadawa mutane hakan.
Daga karshe ta ce ba ta san dalilin da ya sanya ta daina son mijin na ta ba, kuma ba ta son ci gaba da zama a auren da babu soyayya a ciki. Matar ta nemi mutane su ba ta shawara kan hakan.
Cikin masu bata shawara ga abin da wasu suka ce. ki yi kokarin tuno rayuwar da kuka faro tare a baya. daga nan za ki iya cimma matsaya ki ba wa kan ki amsa, amma dai abinda Ubangiji ya yi shine ya fi ba wai zabin ki ba.
Wani ya kara da cewa. Ina mai shawartar ki da ki je hutun sati biyu a wani yanki na kudancin Amurka, ina mai tabbatar miki da cewar soyayyar za ta dawo.”
Shiko RePøßt ce wa ya yi. hidimar iyali akwai wahala. Ina ganin rayuwarki ce, kuma za ki iya gudanar da ita yadda ki ka ga dama, fatan dai kar ki yi da na sani a gaba.”
Pau G kuma cewa ya yi. kawai ki biya shi kudaden da ya kashe hadda kari ma, ki maida masa kudaden da ya kashe miki, daga nan sai ki dawo Najeriya.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahime