Wata mata ‘yar kasar Australia da ta yiwa idonta fentin ‘tattoo’mai launin shudi ta shiga tashin hankalin rasa ganinta, tana kwance a asibiti
Matar mai ‘ya’ya biyar mai suna Anaya Peterson ta kwaikwayi Amber Luke, wata fitacciya ‘yar kwalliya mai shudin idanu
Matar mai karanta ilimin shari’a ta yi dana-sanin kin sauraran shawarin diyarta mai shekaru bakwai kacal
Wata mata mai suna Anaya Peterson ta yi dana-sanin kin bin shawari da gargadin diyarta mai shekaru bakwai da tace kada ta kuskura ta sauya launin idanunta.
An ruwaito cewa, yarinyar ta shawarci uwarta cewa, kada ta sauya launin idonta, hakan zai iya kai ta ga rasa idanun nata gaba daya.
Matar mai karanta ilimin shari’a dai ta kwaikwaiyi wata fitacciya ce, Amber Luke, wacce ‘yar kasar Australia ce da ke launin shudin idanu.
Ita kanta Luke ta sauya launin idanunta ne a shekarar 2019, kuma ta sha fama da makantan wucin gadi na tsawon makwanni uku lokacin da aka yi mata aikin.
Jaridar Daily Mail ta ce, matar mai ‘ya’ya biyar a yanzu haka tana asibiti tun bayan da aka yi mata aikin sauya launin idanu zuwa shudi, domin tana rasa ganinta.
Jaridar ta ce, akwai yiwuwar matar mai shekaru 32 ta rasa ganinta gaba daya duba da yanayin da ta tsinci kanta da kuma tasirin tawadar da aka yi amfani da ita wajen sauya launin idanun.
A baya can, an yiwa Anaya aikin raba harshenta gida biyu tare da yin zane-zane masu yawa a fuska, amma a yanzu ta yanke shawarin sauya idanunta a matsayin sawani sabon salo.
Duk da fuskantar matsanancin ciwon kai da bushewar idanu a matsayin somin waraka, ta yanke shawarin a sake yi ma kanta aikin idon hagu a Disamban 2020.
Bayan watanni ba tare da wata matsala ba, Anaya ta wayi gari wata rana a watan Agustan 2021, inda taga idanunta sun kumbura suntum.
Diyarta ta gargade ta game da aikin sauya launin idanu
Anaya ta bayyana cewa, a tun farko diyarta ta gargade ta game da wannan aikin mai hadari, inda tace yarinyar ta ji tsoron kada ta rasa idanunta gaba daya, CornWallLive ta tattaro.
A yanzu dai Anaya na fuskantar rasa gani, domin idanunta sun fara makancewa a hankali, lamarin da ya tada hankalinta.
A cewarta Da fari na yiwa ido daya ne saboda a tunani na ko da na makanci, akalla ina da sauran ido daya.
“Ya kamata na tsaya haka ne. Diyata ta gargade ni kada na sake yi, tace idan na makance fa? Ita dai bata yarda da hakan ba.”
Rahoton Zuhair Ali Ibrahim.