Mijina ba Shine Uban Ɗa na ba, Amma ban taɓa kwanciya da wani ba, Matar Aure ta koka.
Wata matar aure ta matukar fusata kan sakamakon gwajin kwayar halitta da tayi wa daya daga cikin ‘ya’yanta wanda ta kasa gane dabi’arsa.
Matar ta yanke hukuncin yin gwajin ne domin ta sha waye mahaifin yaron, amma sakamakon ya nuna cewa ba ‘dan mijinta bane.
Wani David Bonbze-Mbir ne ya wallafa labarin Matar a shafinsa Na “Facebook” kuma hakan yasa jama’a sun dinga gurzar kwakwalwarsu don gano bakin zaren.
Labarin wata mata wacce ta musanta kwanciya da wani namiji wanda ba mijinta ba ya bazu a dandalin sada zumuntar zamani na Facebook.
Labarin mai bada mamaki an wallafa shi ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba a shafin wani David Bonbze-Mbir, wanda yace daya daga cikin ‘ya’yan matar ba na mijinta bane.
A labarin, David yace matar ta zanta da shi kan sakamakon gwajin kwayar halittan da tayi wa daya daga cikin ‘ya’yanta.
Sakamakon gwajin DNA ya harzuka matar, Gwajin kamar yadda tace, ya zama dole ganin cewa yaron yana da dabi’a ta daban da sauran yaranta.
Sakamakon gwajin kuwa da ya harzuka matar ya nuna cewa ba mijinta bane uban yaron, Amma kuma abun mamakin shi ne, matar ta musanta taba kwanciya da wani mutum baya da mijinta.
A karshen labarin, David yace: “Saboda mijinta ne namiji daya tilo da ta kasance da shi tun bayan haduwarsu, ta kasa yadda cewa Sakamakon gwajin nan daidai ne kuma ta yaya hakan ta faru.
“Babu wanda zai yarda cewa bata taba kasancewa da wani namiji ba tun bayan haduwarta da mijinta. Ta samu cikin yaron ta yuwu bayan ta auri mijinta amma da wani can daban.
Jama’a sun dinga wasa ƙwaƙwalwa a sashen tsokaci, ana wallafa labarin, jama’a da yawa sun dire akanta, a halin yanzu, ta samu jinjina na sama da 800 tare da tsokaci sama da 1800.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.