Wata Matashiya Wacce Ta Yi Fice A Tiktok Ta Bayyana Gajiyarta Da Rashin Aure.
Shahararriyar jarumar da ta yi fice wajen tikar rawa a TikTok, ta bayyana cewa rashin mijin aure na ci mata tuwo a kwarya
Saudat Shehu wacce aka fi sani da Ummi Darling tace ta gaji da zaman da ta ke yi hakanan babu mijin aure inda ta kosa ta shiga daga ciki
Shahararriyar yar TikTok ta bayyana cewa a shirye ta ke ta tuba daga TikTok domin ta samu mijin da za su yi aure
Shaharrarriyar yar TikTok, Saudat Shehu wacce aka fi sani da Ummi Darling, ta bayyana cewa ta gaji da zama hakanan babu miji sannan a shirye ta ke ta yi zaman aure a matsayin kamilar matar aure.
yar TikTok din wacce ke da kwalin difloma daga jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria, ta yi fice ne a dalilin bidiyoyin rawarta.
A cikin wani bidiyo Ummi Darling ta bayyana cewa tana son ta watsar da harkar TikTok ta yi aure, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
“Ina son na tuba na daina TikTiok saboda ina son na yi aure. Na gaji da zama babu mijin aure. Duk da cewa a yanzu bani da saurayi saboda ban yarda da soyayyar karya ba, sannan ina son na yi soyayya da mutum mai hankali ba yaro ba.”
“Ina son namiji wanda zai dauki nauyin dukkanin dawainiya ta a matsayin matarsa tare da sauke dukkanin nauyin da ya rataya a wuyansa na miji.”
Ummi darling ta yi fice sosai a TikTok shekara biyu da suka gabata saboda baiwar tikar rawar da ta ke da ita.
Tana kiran kanta a matsayin sarauniya wacce ta ke yin rawa kawai a wakokin soyayya duk da a lokuta da dama ta sha bayyana cewa ba ta yarda da soyayya ba.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim