Ya ƙunshe ya gaggen gajeren wando a leda ya baiwa mai abinci ajiya bisani ya ci kwana 2 ya arce.
Ya Kunshe Yagaggen Gajeren Wando A Leda Ya Baiwa Mai Abinci Ajiya, Inda Ya Arce Bayan Ya Ci Kwano Biyu Na Abinci
Wani matashi ya shiga wani shagon abinci, inda aka zuba masa shinkafa da nama, bayan ya kusa cinyewa bai wuce cokali uku zuwa hudu ba, sai ya kafa waya a kunne da zummar yama magana da wani, bayan gama wayar bogin sai ce megidansa ne ya kira a waya kan cewa ya taho masa da abinci a ‘take away’.
Lamarin dai ya auku ne a yammacin jiya a daidai kan titin zuwa asibitin Medical Center dake garin Mararrabar Abuja da jihar Nasarawa.
Bayan an zuba masa, sai ya ce a rufe masa ragowar abinci nasa da yake kan ci, zai dawo yanzu idan ya kammala ci sai ya biya kudin abincin kwana biyu, amma ga ajiyarsa nan a leda yana dawowa.
Bayan mai abinci ta jira shiru bai dawo ba, bude ledan ke da wuya sai ta ga ashe wani fatattaken gajeren wando ne dukunkune a cikin ledan. Wanda hakan ke nufin cewa ya yi garkuwa da wandon ne don ya samu ya dirki abinci a bati siddan.
To wannan kuncin rayuwa ce ta sa shi ya yi hakan, ko kuma dai zamba ne cikin aminci?