Ya Soke Aurensa Da Budurwansa Bayan Kai Ziyarar karshe Ga Saurayinta Da Ta Yi.
Wani Dan Nijeriya Ya Soke Aurensa Bayan Da Ya Gano Budurwarsa Ta Kai Ziyarar Karshe Ga Tsohon Saurayinta.
Bayan rabuwarsu, budurwar ta dauko batun zuwa wani dakin kafar sada zumunta domin neman shawarin jama’a
Ta kuma amsa laifinta cewa, tabbas ta rakashe tare da tsohon saurayinta, kawai ta yi rashin sa’a wanda zai aure ta ya gane
Wata budurwa ‘yar Najeriya ta shiga kunci yayin da saurayin da za ta aure ya ce sam ya fasa, ya soke aurensu.
A cewar wani bidiyon da ya yadu mutumin da zai auri budurwar ya gano yadda ta kai ziyarar karshe wurin wani tsohon saurayinta.
Budurwar, wacce ba a bayyana sunanta ba ta bayyana yadda lamarin ya faru a kafar Facebook, inda ta nemi jin ra’ayoyin jama’a game da lamarin.
Dalilin da yasa ta je gidan tsohon saurayinta a cewarta, ta ziyarci tsohon saurayinta ne domin kai masa katin gayyatar aure, amma aka samu matsala suka aikata badala.
Ta kuma bayyana cewa, da gaske akwai laifinta, amma bata je da niyyar yin lalata da tsohon saurayin ba.
Ta rashin sa’a, domin kuwa mijin da za ta aure ya gano komai bayan da ya datsi manhajar fira ta WhatsApp da budurwar ke amfani ita.
Daga nan, sai kawai mutumin ya ce ya soke duk wani shiri na auren ba tare d abata lokaci ba, ya ma fasa aurenta..
Ta ce a gaba na, ya kira dukkan iyayenmu sannan ya nemi a soke duk wani shirin auren. Lokacin da suka nemi sanin dalili, yace musu zan fi musu bayani da kyau. A nan ya bar ni cikin gidansa ya tafi wani otal kuma Abuja zai koma daga otal din.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim