Wata mata a kasan indiya ta kafa tarihi bayan tayi abinda ake zaton shine bikin aure na farko irinshi a kasan.
Rahotonni sunce matan mai suna Kshama Bindu, mai shekaru 24 ta auri kanta da kanta ne tare da gudanar da bikin auren a gidanta a gaban kawaye da abokan aikinta.
Da farko ta shirya bikin yin auren ne a wani wurin bauta, tare da wani limamin wurin bautan a birnin Badodara, amma shugaban jam’iyyan Bharatiya Janata Sunita Shukla, yayi adawa da bikin auren a wurin bautan.
An fada cewa, a addinin hindu ba’a yarda mace ta auri kanta ba don haka bikin zabai gudana ba.
Sunita tace, ina adawa da zabin wurin don haka ba za’a barta ta auri kanta a kuwane wurin bauta ba.
Irin wannan aure ya sabawa addinin hindu kuma hakan zai rage yawan al’ummar hindu.
Idan wani abu ya sabawa addini, to babu wata doka da zatayi tasiri akan wannan abu injita.amma ga Kshama auren kanta tamkar sa kai ne na tallafawa kanta da kauna marar iyaka.
Da wannan tunanin ta yanke shawaran cigaba da auren kanta kuma ta samu sabon wuri duk da ana jayayya.
Tace, bantaba son yin aure ba amma, inason zama amarya don haka na yanke shawaran auri kaina.
Kshama ta fuskanci kalubalen dakatar da burinta, kamar yadda limamin wurin bautan ya fara shirin yi mata, anyi shirin soke alwashinta tana gab da auren.
A karshe ta samu daman kammala auren kanta ta hanyan bin al’adun “Mehendi da Haldi” nau’in fasahan yin zane a jiki da amfani da hodan Tumeric don gyaran jikita.
A karshe ta shirya tafiya hutun amarcinta a garin Goa bayan an kammala bikin auren kanta da kanta.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.