Yadda Gobara ta tatashi a bankin GT Dake Nasarawa.
Rahotanni sun bayyana cewa wani reshen bankin Guaranty Trust da ke unguwar Mararaba a babban birnin tarayya Abuja ya kone kurmus a safiyar ranar Juma’a.
Kamar yadda rahoton Punch ya ruwaito, reshen GTBank yana kan titin Nyanya da Mararaba a gaban titin Abacha, Karu. Mararaba gari ne mai iyaka a tsakanin FCT Abuja da Jihar Nasarawa.
Da aka tuntuɓi shugaban ayyuka na hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya Abuja, Amiola Adebayo, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ce, “Eh, gobara ta tashi a bankin, amma mun kashe ta.”
Wani rahoto da hukumar kashe gobara ta fitar ya ce gobarar wacce aka kashe da misalin ƙarfe 8:40 na safe, ta tashi ne sakamakon ƙarfin wutar lantarki daga na’urar inverter.
Ya ƙara da cewa gobarar ta tashi ne daga ɗakin sabar da ke dogon bene mai hawa ɗaya .
Rahoton ya ce batura, injin inverter da wasu kayan kayan wuta sune sanadiyyar faruwar gobarar.
Kawo yanzu dai manema labarai ba za su iya tabbatar da ko an samu asarar rayuka ko jikkata mutanen da gobarar ta shafa ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
RAHOTO:- Comrade Yusha’u Garba Shanga.