Yadda Gwamna Ahmad Ya Kai Ziyarar Bazata Ga Asibiti A Cikin A Adai-daita Sahu.
Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato ya kai ziyarar ba zata Asibiti na musamman da ke cikin garin Sokoto a Keke Napep.
Gwamnan ya yi badda kama yayin wannan ziyara ta tsawon awa huɗu kuma ya gano abubuwa da dama
Ya ce mutane sun kai masa korafin mummunar lalacewar da Asibitin ya yi shiyasa ya zabi zuwa ba tare da kowa ya sani ba
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya kai ziyarar ba zata babban Asibiti na musamman a cikin garin Sokoto domin gane wa idonsa yadda ake duba marasa lafiya.
Rahoton Vanguard ya ce mai magana da yawun gwamnan, Malam Abubakar Bawa, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, 2023.
Bawa ya ce mai girma gwamna ya yanke kai wannan ziyara ne bayan korafe-korafe sun cika masa tebur daga mutanen jihar kan rashin ingancin aiki a Asibitin.
Kakakin gwamnan ya ce daga cikin muhimman dalilin da suka tilastawa mai girma gwamna zuwa da kansa sun ƙunshi lalacewar mahalli, rashin wutar lantarki da lalacewar kayan aikin da na gwaje-gwaje.
Ya kara da cewa gwamna Aliyu ya kai wannan ziyara ne a Keke Napep domin ya tattara bayanai masu muhimmanci daga ma’aikatan asibitin da kuma marasa lafiya.
“Na sha mamakin abinda idona ya gani yayin ziyarar awa huɗu da na kai Asibitin, naga komai da kaina. Marasa lafiya da masu jinya na cikin wani hali a mahalli mai datti kuma ga rashin kayan aikin malaman Asibiti.”
“Yan uwan marasa lafiya sun koma nema wa kansu haske saboda lalacewar wutar lantarki a Asibitin. Na umarci shugabannin Asibitin su zo mu zauna mu ga yadda za’a farfaɗo da Asibitin.”
Wata babbar mejinya a cikin masu gudanarwa na Asibitin ta shaida wa hukumar dillancin labarai ta kasa (NAN) cewa gwamnatin da ta gabata ce ta jawo lalacewar Asibitin.
A cewar majiyar, haka kurum tsohuwar gwamnati ta daina turo kasafin gudanar da Asibitin na wata-wata kuma hakan ya jawo komai ya zama sai Addu’a, rahoton Gazettengr ya tattaro.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.