Yadda jawabin taron ci gaba na kungiyoyin Arewa ya ja hankalin yan Najeriya.
Jawabin Bayan Taron Yini Guda Na Masu Ruwa Da Tsaki Don Tattauna Muhimman Batutuwan Da Suka Shafi Ci-gaban Arewa Tare Da Masu Ruwa Da Tsaki Na Kungiyoyin Cigaban Al’umma A Arewa House Kaduna.
JIGO: TAFIYA DA KOWA DON DAUREWAR DIMOKARADIYYA
Muna masu mai da hankali akan ya waitar damuwa da ke tasowa nan da can, tun bayan 25 ga watan biyu, na shugaban kasa da majalisun tarayya, in da aka samu gabatowar sabbun shugabanni.
Kungiyar Democracy Watch Initiative ta shirya taron wuni guda don tattauna muhimman batutuwa a Kaduna.
Jigon taron shine: Tafiya Da Kowa Don Daurewar Dimokaradiyya a karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattijai, Dr. Abubakar Bukola Saraki.
Gabobin da bayanin bayan taron ya kunsa wanda masana daban-daban suka gabatar daga daukacin yankunan Arewacin Najeriya gasu kamar haka:
JAWABIN BAYAN TARO
1. Mun hakikance ba wani salon gudanar da gwamnati da yafi dimokaradiyya, ba wata sahihiyar hanya ta Samar da shugabanni sama da ingantaccen zabe.
2. Mun hakikance cewa kokarin cusawa majalisa ta goma shugabanni da ake da kokonton kwarewar su. Hakan karen tsaye ne ga ‘yancin majalisa na cin gashin kanta da karya ka’idojin aikin majalisa na fayyace aikin kowa tsakanin majalisun dokoki da na zartarwa, da bangaren shari’a.
3. Masu ruwa da tsakin sun baiyana mamakin ganin yanda jam’iyyar APC ta manta cewa shugabancin jam’iyyar da zaben fidda gwani na cikin gida duka sun gudana ne ta hanyar zabe. Amma sai ga shi jam’iyyar na kokarin cusawa majalisu shugabanci ta hanyar magudi da tauye hakki.
4. Taron yayi Allah wadai da yanda shugabancin APC karkashin Abdullahi Adamu suka dage sai sun yi murdiya sun saka wanda suke so ya shugabanci majalisar ta dattijai.
5. Taron yayi la’akari da yanda yankin Arewa ya samar da kuri’u masu mahimmanci da suka tabbatarwa da APC nasara a zaben shugaban kasa duk da cewa dan takarar ya fito daga yankin kudancin kasar nan ne.
7. Taron yayi na’am tare da la’akari da cancantar Arewa da ta samu tagomashin gudummawar da ta bada da kwantar da kai da mutanen yankin suka nuna.
8. Don haka muna kira da karfafa gwiwa ga duk mai neman wani mukami daga kowanne yanki yake, da su nema, su kuma dage sai anyi zabe.
9. Muna masu Jan hankali da a bawa Abdul’Aziz Yari da sauran masu neman mukami damar su da kundin tsarin mulkin kasa ya basu da su nema tare da sauran masu bukatar shugabancin majalisar daga kudancin kasar nan.
10. Abbas Tajuddeen da sauran masu neman mukamin kakakin majalisar kasa daga Arewa su zage dantse su nemi kujerun su ta hanyar zabe.
11. Muna fatan za ayi la’akari da cancanta, kwarewa da gogewa wajen zaben shugabannin majalisun, sannan wadanda suka fadi, su rungumi kaddara tare da aiki da wadanda suka ci, don ganin an ciyar da kasar nan gaba
12. A karshe taron ya ja hankalin zababben shugaban kasa mai jiran gado Ahmed Bola Tinubu da kada ya sakankance da masu jiran dama daga wajen sa, masu yunkurin samar da wani sabon rukunin ‘yan gaban fada, wadanda yanzu haka suke masa ingiza mai kantu ruwa akan bukatun fifita yanki da tsohuwar al’adar jefa majalisu a alhajin shugaban kasa.
13. Muna fatan zababben shugaban kasa zai maida hankali wajen kokarin daga darajar sa a idanun al’ummar kasar nan, da dawo da darajar gwamnati da kokarin tabbatar da ginshikan da zasu sa dimokaradiyya ta daure, da girmama kundin tsarin mulkin kasa da kokarin kaucewa raina zabin majalisun akan kan su.
14. Taron ya yarda zai mika wannan rubutaccen bayanin bayan sako ga zababben shugaban kasa da jam’iyyar sa ta APC.
Nagode
Sa Hannu:
Shugaban Kwamitin Bayanin Bayan Taro
Dr. Muhammad N. Bello Da Nasiru Abdulkadir Dambatta.