Daga Zuhair Ali Ibrahim
“A Daren jiya Lahadine masu garkuwa da mutane suka shiga wani Anguwa da ake kira da Anguwar Sarkin rafi dake bayan asibitin ƙofar gayan na Gambo Sawaba cikin birnin Zariya inda suka tattara Mutane 8.
ALFIJIR HAUSA ta samu halarta zuwa cikin wannan Anguwar da lamarin ya faru, inda wakilanmu suka samu damar zantawa da ɗaya daga cikin wanda ya kuɓuta daga hannun su masu garkuwa da mutanen.”
“A cigaba da zantawar mu da shi Aliyu Umar wanda aka fi sani da (Ɗan lami), ya tabbatar mana cewa masu garkuwa da Mutanen sun taresa ne da wurin misalin ƙarfe 10 da kwata na dare, a cikin su wasu sanya da kakin sojoji suka taresa yana kan hanyarsa ta komawa gida.”
Bugu da ƙari bayan sun kamasa sai suka ɗaure hunnunansa, sai dai a lokacin da suka kamasa ɗin ya tarar da akwai wasu mutane uku da suka kama akwai wasu mata da miji da kuma wani wanda bai san saba to a cikin haka sai aka kira wayansa, bayan ankira wayarsa sai suka katse kiran suka kashe wayar suna tabbaya ina ne gidansa yake ? kuma menene sana’arsa ? to da ya gaya musu cewa shi kafin tane sai suka ce to za su gidansa.”
Ana cikin haka sai wani daga cikinsu yayi mai magana amma da yare sai yaga ya kyalesa da tambaya, can kuma sai yaga an kawo wasu mutane uku tare da wani Alaramma, sai suka zama su takwas camma sai suka ƙara kawo wani daga nan ne suka zama su tara, sai suka ɗaure hannayen kowa a cikinsu suka tasa su gaba Ni dai ina karanta abin da Allah ya horemasa da ya iya daga bakinsa.”
Ɗanlami ya cigaba da bayani kamar haka, daga cikin masu garkuwa da mutane ɗin su takwas ne, uku ɗauke da Adduna Biyar ɗauke da bindigu kuma duk cikarsu basu wuce shekaru 20 20 ba.”
Har wala yau a cigaba da zantawarmu da shi ɗin yaka da baki inda yake cewa domin wallahi In da ba din bindigar hannun suba duk wanda ya buga babu mai iya tashi cikin su, ana haka bayan sun ta sa su a gaba sai ya fara murɗe hannuwansa har ya iya kwancewa amma sai bai nuna musu cewa ya kwance ba ya rike igiyar to bayan sunzo dab da wata gonar dawa sun raɓeta kawai sai ya yi cikinta a guje wasu daga cikinsu suka bi shi yana gudu yana faɗuwa da haka dai har Allah ya tsirartar da shi.”
Hoto: Barr Nuraddeen Isma’eel.