Yadda Matar Aure Ta Kama Mijinta Da Mata 8 Rigis Suna Gogewa Juna Raini A Shimfiɗarsu.
Yadda na kama mijina yana lalata da mata 8 akan gadona matan aure ta koka.
Wata matan aure ta shaidama duniya halinda take ciki ita da mijinta a unguwan agege dake birnin lagos.
Matan wacce muryanta yadinga yawo a kafan sada zumunta ta tiktok, inda ‘yan mata suka dinga kwaikwayon muryanta a lokacin data ritsa mijinta da mata yana lalata akan gadonsu na aure.
Matan tayi bayani dalla dalla,inda tayi bayani a gaban kotu.
A cewanta mijinnata bayi aikin baki balle na fari, sai shaye-shaye da bin mata amma a wannan karon abinya ta’azzara don ta dawo daga tallan magungunan kwari da take sayarwa kwatsam saita ritsa shi da mata 8.
Tace shigarta dakin keda wuya saitaji sautinsa da matan.saita karasa ciki taganshi da mata har 8 yana canji kamar yadda ake canza zannuwa.
A cewanta, mamaki ne ya kamata hakan yasa ta nemi jin wannan ba’asin saiya gaura mata mari tare da cemata kada ta dinga shiga harkokinshi da basu shafeta ba.
Matan ta bayyana yadda ta tattare kayanta ta tafi gidan iyayenta tare da yaranta biyu wanda dama itane take kula dasu,inda ta barshi shida wadannan matan.
Daga bisani ta amsa gayyatan kotu,inda alkali ta nemi jin ta bakinta bayan mijinta yakai karanta wanda ta shaidama alkali cewa mata 8 ta kamashi dasu a gadon aurenta.
A nan ne alkalin ta yadda su shirya amma duk da haka abin yaci tura.
Wanda yanzu haka basa tare kuma tana cigaba da lallaba rayuwanta cikin kwanciyan hankali da walwala.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.