Yadda taron Democracy Watch Initiative a kaduna ya kayatar da al’ummar Arewa.
Taron Democracy Watch Initiative A Kaduna Ya Ɗauki Hankalin Dubban Mutane A Arewacin Najeriya.
Dole ne abar demokradiyya tayi aiki wajen zaben shubannin majalisa ta goma (10) a cewar Dr Hakeem Baba Ahmed, Dr, Sadiq Gombe Dr Usman Bugaje, Prof Abubakar Jika Jiddere da kuma Prof Abubakar Aliyu.
Tun da safiyar yau Alhamis ne mabanbanta mutane daga sassa daban-daban na arewacin Najeriya su ka hallara a babban ɗakin taro dake Arewa House a jihar Kaduna, domin tattaunawa tare da zaƙulo hanyoyin da za su ƙara bunƙasa Arewacin Najeriya ta fuskar cin moriyar demokradiyya da shan romanta.
Yayin taron malamai daga manyan jami’o’i daban-daban ne suka halarci taron kuma suka gabatar da muƙaloli da yawan gaske, sai dai Prof. Abubakar Jika Jidjere ya yi sharhi akan irin gudunmawar da Arewacin Najeriya take bayarwa wajen ganin samun nasarar kowanne ɗan takarar shugaban kasar Najeriya, inda a wannan zaɓen kusan zaɓaɓɓen shugaban kasar Najeriya ya samu kusan 25% a kowacce jiha da ke Arewa, wannan ke nuna ƙarfin Arewa cin Najeriya tare da irin gudunmawar da yankin ke bayarwa.
Dr, Sadiq ya jaddada kiransa ga al’ummar arewacin Najeriya da su tashi tsaye, yanzu lokaci ya wuce da za su rinƙa zuba idanu suna kallo ba tare da sun mori romon demokradiyyar da suka zaɓa da kansu ba, domin ita demokradiyyar ma domin al’umma take gudana ko take wanzuwa.
Wajibi ne al’ummar arewacin Najeriya su miƙa su rinka duba duk abinda ya ta so ta fuskar demokradiyyar domin ganin yankin Arewa ya samu gwaggwaɓan kaso mai ƙarfi duba da irin gudunmawar da mutanen yankin suke bayarwa wajen nasarar kowanne zaɓaɓɓen shugaban kasar Najeriya.
Daga karshe anyi kira ga zaɓaɓɓen shugaban kasar Najeriya da ya bari demokradiyya tayi aiki wajen Zaɓen wanda zai wakilci majalisar dattijai ta goma, haka-zalika a dukkan abinda ya shafi siyasa da demokradiyyar domin wannan abubuwan sune suka kawo shi zuwa matakin nasarar da yake kai.