Yadda uba ya siyar da dansa ga masu siyan mutane akan 150,000.
Daga: Shoaibu Shehu (Young Author)
Daniel Chigozie, me kimanin shekaru 30 a duniya, ya karbi kudi kimanin Naira 150,000 a karo na farko, daga bisani ya sake sayar da ɗan nasa a kudi Naira 400,000, bai dandara ba ya sake karban 700,000, wannan cinikayya anyisu ne tsakanin August 2022 zuwa February 2023.
Daniel wanda dan asalin Abela Sango Ota, na karamar hukumar Ado-Odo/Ota na Ogun state. Jami’an hukumar Amotekun sun cika hannu dashi bayan zargin siyar da dansa dan wata tara ga mutane mabanbanta, masu siyan mutane.
Komandan Amotekun na jihar Ogun, David Akinremi ya bayyanama manema labarai cewa rundunan binciken manya laifuka na Hukumar sunyi nasaran tsafke uban bisa cefanar da dansa Daniel Chinonye Darlington ga masu harkallan mutane a wajaje mabanbanta da suka hada da Sango, Meiran da kuma Apapa na jihar Legas.
Akinremi ya kara da cewa, Daniel dan kungiyan asiri ne kuma yana amfani da siddabaru wajen dawo da ɗan nasa daga waɗanda suke siyansa.
Wanda ake zargin ya amsa lefinsa yayin da hukumar yaki da safarar mutane suka kai ziyara a hedkwatar hukumar ta Amotekun. Hukumar ta National Agency for the prohibition of trafficking in humans ta dukkufa don cigaba da bincike don yankema Daniel hukunci data dace dashi.
Allah ya tsare.