Yadda Wani Mai Tukin A Dai-daita Sahu A Zariya Ya Yi Dakon Manyan Mata 10 A Baya.
Wani Matashi Mai Keke Napen Ya Yi Sanadiyar Sanya Wata Yar Son Banza Yin Fitsari A Jiki.
Wani matashi mai tukin Keke Napen ya kusa halaka wasu mata da ya ɗakko a Keken mai kafa uku daga Sabon Garin zuwa birnin Zariya.
A Yammacin Ranar Laraba wani mai tukin Keken Napen da ya ɗanko fasinja daga sabon garin zuwa kofar doka idan wannan shirin da mai keke Napep din ya yi ya sabawa ka’ida.
Matan Biyu yan kabilan yaroba sun tsaida mai abin hawan inda ɗaya daga cikinsu ta ce za ta sauka a kofar doka daya kuma tudun wada sai dai duk da girmansu amma sun kasa biyan asalin kudin da ake dauka.
Daya daga cikin matan Allah ya yalwata mata kiba sosan gaske dayar kuma bata kai ta kina ba mai kibar wacce ita ce za ta sauka kofar doka bisani dayar a tudun Wada.
Sai dai mai Napen din ya nuna rashin jin dadin sa domin ya yi tunanin mai girman jikin ba za ta nemi sauki bai sai ta nemi rage a yanda ake zuwa akan za ta ba da Dari da 30 dayar kuma Naira dari a haka ya danko su.
Shigar su cikin motar sun tarar da wani fasinja in da suka nemi ya matsa musu bayan matsa suka kara neman ga matsa har sai da fasinjan nan suka man nesa jikin karfe Napen.
Ganin hakan sai mai Napen din ya dinga zuba gudu kamar ya sato su sai dai matan sun kasa jurewa suna ta mai ihu ya rage gudu tun da ba sauri su ke ba.
Jin hakan matakin ya dauki niyar sai ya shiga Zaria a cikin mintinan 15 duk da sai an shafe mintina 40 ana tsola tafiya daga sabo zuwa Zaria.
Wakilin Jaridar ALFIJIR HAUSA wanda lamarin ya faru a gabansa ya shaida mana cewa cikin matan akwai wacce sai da ya kwarara fitsari a jikinta saboda fargaban mai ka iya zuwa ya dawo.
Jin kadan bayan saukar dayan wacce za ta sauka a tudun Wada ta biya kudinta tace kar Allah ya kara hada ni da kai sai ya rage wannan mai cin kujerar mutun biyun ne a ciki Napen din.
Da ya fahimci ta fi jin tsoro sai ya kirkiri sabon wulakanci tuki in da ya ke kutsawa kai tsaye ba tare da lura ba ko duba hanya har sai da ta kara tsula fitsari a jiki ta na mai yi masa magiya.
Rahoton ya nuna matar ko karasa wa in da za ta sauka ba ai ba ta ce a tsaya ta sauka sai dai mai Keken ya nimi kin tsayawa ya ce ai ya san in da ta ke sauka dan haka sai ya kai ta har wajan.
Wakilin mu ya kara shaida mana cewa ko da a ka zo wajan saukar na ta ko tsawa ansan chanji ba tai ba ta kira wani almaji domin ya amshi chanji in da ta nufi hanya gida tana zage zage.
Mai Napen din ya bayyana dalilin da ya sa ya yi haka, a inda yake bayyana mana cewa matar ta na da son banza shi kuma ya yi alkawarin sai ya yi maganin son banzan ta domin nan gaba ta gyara halin ta duba da yanda farashin man fetur ya kara kuɗi.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.