Yadda Wata Babban Mota Ta Afkawa Masallata Har Cikin Masallaci A Jihar Neja
A safiyar ranar Talata ne wata babbar mota ta kutsa kai cikin wani masallaci a garin Suleja na jihar Neja, inda mutane uku ciki har da wani yaro ya samu munanan raunuka.
A cewar wani ganau, Usman Haruna, wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 6 na safe, inda akasarin masallatan da suka taru domin yin sallar asuba suka watse.
“Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 6 na safe inda mutane da dama suka fita daga masallacin bayan sallar asuba, wasu kadan ne suka rage domin kammala addu’o’insu a lokacin da motar ta fado a sashin baya na masallacin.
“Motar ta fado ne a lokacin da direban ya yi kokarin kunna wata karamar hanya kusa da masallacin.
Ya ce masallatan da suka makale a cikin rugugi sun hada da mata da wani yaro, inda ya kara da cewa tirelar ta fado ne a bangaren baya na masallacin da mata da kananan yara ke sallah.
“Mutane uku, ciki har da wani yaro, sun makale a cikin baraguzan ginin, amma daga baya an ceto su kuma an kai su babban asibitin Suleja domin yi musu magani.”
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida.