Yadda wata mata ta sayarda mahaifiyanta ta sayi kayan daki a Borno.
Wata dattijuwa mai suna yabi Ahmed, ta bayyana ma duniya yadda ‘yarta ta cikinta ta saida ita ga masu yankan kai domin tayi kayan daki.
Matar wacce tace ita haifaffiyan garin kano aure ne yakaita garin Maiduguri, inda ta haifi yara guda uku biyu maza da kuma mace daya.
Tace,tana zaune da yaranta cikin maraici bayan rasuwan mahaifinsu Malam ado,inda ta aurar da ‘yarta mace guda daya su kuma sauran mazan tana tare dasu suna makaranta zasu kaiga yin aure ba.
Yabi ta shaidama manema labarai cewa, wata rana tana zaune a gida ita daya saiga yarinyanta ta gidan aure tayi sallama.ta amsa sallama saitaga ‘yarta cikin tashin hankali.
Tace tambayi yarinyan meya faru da ita saitace mata babu lafiya mijinta ne zaiyi mata kishiya yakeyi mata wulakanci,amma kizo muje kiga irin wulakanxin da yakeyimin.
Kasancewan ita daya nake da ita mace don haka banason abinda zai sameta nasaka hijabina muka tafi.
Yabi tace maimakon muje hanyan gidanta sainaji tana fadama dan adaidaita yakaimu wata unguwan daban.
Nace a ina mijin naki yake saitacemin a wajen da yake neman auren zamuje musamoshi, har zanki zuwa tunda ni suruka ne gara musameshi a gida sam ‘yata taki yadda kasancewan bancika yimata musuba saboda irin kaunan da nakeyi mata sai muka tafi badan naso ba.
Mukaita tafiya harmuka fara zuwa bayan gari saitace ma mai adaidaita ya tsaya munzo ta sallameshi mukuma muka nufi wata mota tacemin mijinta ne a cikin motan muje gunshi kai tsaye.
Muna zuwa jikin motan saina ganni a wani guri na daban, inda naga wasu mutane da bansansu ba bankuma taba ganinsu ba nayita dubawa sainaga babu ‘yartawa a gurin babu wanda yake magana da dan uwanshi.
Tace a haka na wuni na kwana saina fara ‘yan addu’o’in da suke bakina