Yadda yaro ya lakadama mahaifinshi duka bisa zargin satan mishi ganyen kuka a Bauchi.
Wani yaro mai suna faisal ya lakadama mahaifinshi dukan kawo wuka saboda uban ya zarge shi da sace mishi ganyen bishiyan kuka.
Wata majiya ta shaidama mana cewa, uban yasha dakyar a hannun danshi, inda ya caccaka mishi wuka saboda ya zargeshi da kwashe mishi ganyen kuka da ya ajiye wanda yakai kimanin naira dubu goma.
Majiyan tace, uban ya dade yana zargin dan nashi da yi mishi sace sace inda wannan karo ya kamashi dumu-dumu da laifin sace mishi ganyen kuka.
Mahaifin yaron mai suna Malam Bala, dake zaune a unguwan makwalla, a cikin garin bauchi ya saba saro ganyen kukan a gona yana tarawa ya sayar kamar yadda ya saba.
Kwatsam sai ya wayi gari yaga babu duk ganyen, inda yake zargin cewa danshi ne ya kwashe.
Malam bala ya kira yaron domin tambayan shi yadawo mishi da ganyen, sai yaron ya fara zagin uban yana nunashi da yatsa.
Yahaushi da duka da zagi, inda yaron ya zaro wuka ya caccaka ma mahaifin nashi.
Bayan faisal ya caka ma mahaifinshi wuka yaganshi cikin jini saiya gudu, ya tsere inda haryanzu za’asan inda ya boye ba.
Wanda yanzu haka Malam Bala yana babban asibitin koyarwa da ke garin bauchi yana jinyan raunin.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.